Duck hunt
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
RAMUWAR AZUMI

Ali Khamenei4

T808: Na sha ruwan azumi na kwanaki sha takwas saboda tafiyar da na yi cikin watan Ramalana don aiwatar da wani aiki na addini, to mene ne hukumcin da ya hau kaina? Shin wajibi ne in rama su?

A: Rama azumin watan Ramalana da ka sha saboda tafiya wajibi ne.
809: Mutanen da tafiya ta kama su cikin watan Ramalana saboda wani aiki na addini, saboda haka ba za su iya yin azumi ba. To idan bayan wasu shekaru suna son rama wadannan azumi da suka sha, to shin bayar da kaffara ya wajaba a kansu?

A: Idan har jinkirin rama azumin zuwa wata shekarar ta daban ya samo asali ne sakamakon ci gaban uzurin da ya hana mutum daukan azumin, to rama azumin da ya wuce din kawai ya wadatar, ba wajibi ne ba ne ya ciyar da mudu guda ga miskini a madadin kowace rana, duk kuwa da cewa bisa ihtiyati ana son a hada biyun. To amma idan rashin ramuwar ta samo asali ne sakamakon sakaci ba tare da wani uzuri ba, to hada ramuwa da ciyarwar wajibi ne.
811: Wani mutum ne ya yi shekaru goma saboda jahilci ba ya salla da azumi. To a halin yanzu sai ya tuba ya koma ga Allah, don haka sai ya dauki aniyar rama wadannan ibadu da ya bari. To amma sai dai ba shi da karfin biyan dukkanin azumin da ya sha sannan kuma ba shi da kudin da zai biya kaffaransu. Shin ya halalta ya takaita kawai da yin istigfari?

A: Ramuwar azumin da mutum ya sha ba sa faduwa daga kansa ta ko ta wani irin yanayi. To sai dai dangane da kaffarar karya azumin watan Ramalana da gangan to matukar ba shi da karfin yin azumin wata biyu ko ciyar da miskinai sittin ga kowace rana, to wajibi ne ya ciyar da miskinan da zai iya sannan kuma bisa ihtiyati ya ci gaba da yin istigfari. Idan kuwa ba shi da karfin komai kashin ciyarwa to yana iya wadatuwa da yin istigfari da zuciyarsa da harshensa yana cewa: Astagfirullah.
812: Sakamakon rashin karfi na kudi da nake fama da shi na gagara sauke nauyin kaffaran da ke kaina na azumi ko kuma ciyar da miskinai, don haka daga karshe dai abin da na yi shi ne istigfari (neman gafarar Ubangiji). To amma cikin ikon Allah a halin yanzu na samu karfin yin azumin ko kuma ciyar da miskinan. To me ya kamata in aikata?

A:A irin wannan hali yin kaffara ba wajibi ba ne, ko da yake ihtiyati mustahabi shi ne a yi hakan.
813: Mene ne hukumcin mutumin da ya jinkirta rama azumin dake kansa har wani azumin ya zo saboda jahilcin da yake da shi kan hukumcin wajibci rama azumi kafin wani watan azumin ya zo?

A: Jahiltan hukumcin jinkirta ramuwar azumi har zuwa wani azumin ba ya sanya kawar da wajibcin kaffaran hakan wato ciyar da miskini mudu guda a madadin kowace rana.
815: Na yi azumi ne na kimanin wata guda da niyyar cewa idan har ina da wani azumin da ban yi ba to wannan azumin ya zamanto ramuwar wancan azumin. Idan kuwa ba ni da wani azumi a kaina to ya zamanto saboda neman kusanci da Allah kawai. To shin ana iya kirga wannan azumi a matsayin ramuwar azumin da ke kaina (idan har akwai)?

A: Matukar yayin niyyar azumin ka kudura aniyar sauke nauyin dake kanka ne na ramuwar azumi ko kuma na mustahabi, sannan kuma ya zamanto kana da azumi a kanka da za ka rama, to za a kirga shi a matsayin ramuwar azumin.
816: Mutumin da bai san yawan azumin ramuwar da ke kansa ba, to idan har aka dauka yana da azumin ramuwa a kansa sai kuma ya yi azumin mustahabi, amma shi kuma yana jin cewa ba shi da azumin ramuwa a kansa. To shin za a kirga wannan azumi nasa (na mustahabi da yayi) a matsayin biyan azumin dake kansa?

A: Ba za a kirga azumin da yayi da niyyar mustahabi a madadin azumin ramuwar da ke kansa ba.
: 817: Mene ne hukumcin mutumin da ya karya azuminsa saboda jahiltan hukumcin? Shin ramuwa ce ta hau kansa ko kuma har da kaffara?

A: Matukar hakan ya faru ne saboda jahiltan hukumcin da yayi sannan kuma babu wata gajiyawa da ya nuna wajen sanin hakan, to ramuwa ce take kansa kaffara ba wajibi ba ne.
818: Wanda a farko-farkon balagarsa ya gagara yin azumi saboda rauni da rashin iyawa, to shin ramuwa ce ta hau kansa ko kuma har da kaffara bayan ramuwar?

A: Matukar babu wata wahala tattare da daukan azumin gare shi amma duk da haka ya sha ruwa da gangan, to bayan ramuwa wajibi ne ya yi kaffara. Amma idan har akwai tsoron cutarwa gare shi idan har ya dauki azumin, to ramuwa ce kawai ta hau kansa.
819: Mene ne hukumcin mutumin da bai san adadin azumin da ya sha ba da kuma yawan sallar da bai yi ba? Sannan kuma mene ne hukumcin mutumin da bai san shin shan azumin da yayi bisa wani uzuri na shari'a ne ko kuma da gangan kawai ya sha azumin ba?

A: Zai iya takaita kawai da ranakun da yake da yakinin ya sha azumi a cikinsu haka nan ma sallolin da bai yi din ba. Idan kuma yana shakkan kan ko da gangan ya sha ruwan ko kuma a'a, to ba wajibi ba ne ya yi kaffara.
820: Mene ne hukumcin mutumin da bai tashi don yin sahur ba, don haka ya gagara kai azuminsa har zuwa faduwar rana, wato a tsakiyar rana ya karya azumin nasa?

A: Matukar dai yin azumin zai zutar da shi (cutarwar da shari'a ta yadda da ita) don haka ya gagara cika azumin, to ramuwa ce ta hau kansa. Kaffara ba wajibi ba ne a gare shi.
823: Mutumin da likita ya ce masa yin azumin zai cutar da shi saboda rashin lafiyan da yake fama da shi, don haka sai ya ki daukan azumi. To amma bayan wasu shekaru sai ya gano cewa yin azumi a wancan lokacin ba zai cutar da shi ba, likitan kawai ya yi kuskure ne wajen gano hakikanin lamarin, to shi ramuwa da kaffara sun hau kansa ne?

A: Matukar dai shan ruwan da yayi din ya samo asali ne daga fadin likitan da aka yarda da shi ko kuma ya samo asali ne daga abubuwan da hankali ya yarda da su, to ramuwa ce kawai a kansa.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din