BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
GANIN WATA
T834: Kamar yadda dai ka sani ne cewa yanayin jinjirin wata a karshensa (ko kuma a farkonsa) ba ya fita daga daya daga cikin wadannan halaye:
(1): Buyan wata ta kasance kafin faduwar rana.
(2): Buyan wata ta kasance dai-dai da faduwar rana.
(3): Buyan wata ta kasance bayan faduwar rana.
To muna so ayi mana bayanin wadannan al'amura:
Na farko: A cikin wadannan halaye guda uku, a mahangan fikhu wanne ne a ke daukansa farkon wata.
Na biyu Idan muka yi la'akari da cewa dukkan wadannan halaye guda uku a kan iya gano su ta hanyar naurori da suke yin wannan aiki to shin ana iya amfani da wannan na'ura wajen gano farkon wata, ko kuma dai wajibi ne sai an gan shi da ido?
A: Abin la'akari dangane da farkon wata shi ne watan da yake buya bayan faduwar rana, wanda za'a iya ganinsa kafin faduwar rana ta yadda aka saba. Matukar mukallafi bai sami yakini ba dangane da lissafi na ilimi, to hakan ba shi da wata kima, wato ba abin dogaro ba ne.
836: Idan ba a ga watan Shawwal a wani gari ba, to amma gidan radiyo da talabijin suka ba da sanarwar ganin wata, to shin hakan yana wadatarwa ko kuma dai sai an kara bincike?
: Matukar aka sami tabbacin kamawar watan ko kuma Waliyul Fakih ne ya ba da sanarwar ganin watan, to hakan ya wadatar ba bukatar a ci gaba da bincike.
838: Shin haduwar ufuki sharadi ne na ganin wata ko kuma a'a?
A: Ganin wata a garuruwan da suke da ufuki daya ko kuma suke kusa da juna ko kuma a garuruwan da suke gabashi ya wadatar.
841: Idan aka samu sabani tsakanin maluman wani gari dangane da ganin wata da kuma rashin ganin sa, kuma adalcin wadannan malamai dukkansu ya tabbata ga mutum, kuma yana da yakini kan bincike da bin diddigin kowane daya daga cikinsu, to mene ne ya wajaba ya aikata?
A: Idan har wannan sabani nasu kan korewa ne da kuma tabbatar (da ganin watan) kamar wasunsu su yi da'awar tabbatar watan kana wasu kuma su yi da'awar tabbabar da rashin tsayuwarsa, to hakan karo ne tsakanin hujjojin guda biyu, to a wannan hali sai mutum ya jefar da dukkan wadannan maganganu biyu, ya koma ya yi riko da abin da shari‘a ta tabbatar na yin aiki da asali daga usul, wato kamar babu wadannan maganganu. To amma da sabanin nasu ya ta'allaka ne da tabbatarwa da kuma rashin masaniya kan tabbatuwan (ganin watan), kamar wasunsu su yi da'awar ganinsa wasu kuwa su ce su ba su gan shi ba, to maganar wadanda suka ce sun gani idan dai adilai ne shi ne abin riko a shar'ance ga mutum, kuma wajibi ne ya bi hakan, haka kuma da Hakim al-Shar'i zai bayar da sanarwar ganin watan, to hukuncinsa hujja ce ga dukkan mutane, kuma wajibi ne su bi shi.
848: Shin farkon watan Ramalana mai alfarma da kuma karshensa yana tabbata ne da ganin watan ko kuma ta hanyar kalanda, ko da kuwa watan Sha'aban bai kai kwanakin talatin ba?
A: Ana tabbatar da farko ko karshen watan Ramalana ne ta hanyar ganin (watan) mukallafi ko kuma da shahadar adilai biyu ko kuma da yaduwar labarin da babu shakku cikinsa ko kuma da cikan kwanaki talatin ko kuma da hukumcin Hakim al-Shar'i.
849: Idan ya halatta a bi abin da wata hukuma ta sanar dangane da ganin wata, kuma wannan sanarwa ta kasance wani mizani na tabbatuwan ganin wata a wasu garuruwan, to shin wajibi ne wannan hukuma ta zama ta Musulunci, ko kuma za'a iya amfani da hakan ko da kuwa hukuncin ya fito ne daga hukuma azzaluma fajira?
A: Abin la'akari kawai shi ne samuwar nitsuwa kan ganin watan a wannan guri.
731: Yarinyar da ta kai shekarun balaga, amma saboda raunin jikinta ba za ta iya yin azumi ba haka nan bayan watan Ramalanan ma ba za ta iya rama azumin da ta sha din ba har wani watan na Ramalana ya shigo, to a nan mene ne hukumcinta?
A: Rashin samun damar daukan azumi ko ramuwarsa saboda kawai raunin jiki ba ya kawar da wajibcin ramuwar azumin. Don haka wajibi ne ta rama wadannan ranaku na azumi da ta sha.
732: Yarinyar da ta kai shekarun balaga sannan kuma yin azumi gare ta ya zama da dan wahala, to a nan mene ne hukumcinta? Sannan kuma shin balaga ta shari'a ta ‘ya mace shi ne cikan shekaru tara na hijira kamariyya?
A: Bisa ga maganar da ta fi shuhura, balagar ‘ya mace shi ne cikan shekaru tara na hijira kamariyya, wanda a wannan lokacin azumi wajibi ne a kanta sannan kuma barinsa saboda wasu ‘yan dalilai ba ya halalta. To amma idan har yin azumi zai cutar da ita ko kuma ba za ta iya jurewa ba, to ya halalta ta sha ruwa.
733: Ni ban san takamammen lokacin balaga na ba, don haka ina son mai girma yayi min bayani dangane da lokacin da daga shi ne zan fara biyan salloli da azumin da ban yi ba. Sannan kuma shin kaffara ta hau kaina ko kuma saboda rashin masaniya ramuwa ce kawai a kaina?
A: Za ka rama gwargwadon salloli da azumin da kake da yakini sun wuce ka ne bayan cika shekarun balaga. Amma dangane da azumi idan har akwai gazawa daga bangarenka wajen gano hukumcin shari'a, shi ya sa ka sha ruwan, to bayan ramuwa akwai kuma kaffara a kanka.
734: Yarinyar da ta cika shekaru tara azumi ya wajaba a kanta, to amma saboda dalili na tsanani sai ta karya azuminta, to shin wajibi ne ta rama wannan azumi?
A: Wajibi ne ta rama azumin watan Ramalanan da ta sha.
735: Idan mutum saboda wani uzuri mai karfi, kashi hamsin cikin dari sai ya yi zaton cewa lalle azumi ba wajibi ba ne a kansa don haka sai ya sha ruwa. To amma daga baya sai ya fahimci cewa lalle azumi ya wajaba a kansa. Wani hukumci ne ya hau kansa (na ramuwa da kaffara)?
A: Idan ya sha ruwa cikin watan Ramalana da gangan saboda kawai zaton rashin wajibcin azumi a kansa ne, to a irin wannan yanayi na tambayar baya ga ramuwa wajibi ne ya yi kaffara. Amma idan har ruwan da ya sha din ya samo asali ne saboda tsoron cutarwa da yake wanda kuma ya ginu ne bisa asasi na hankali, to kaffara ba ta zama masa wajiba ba, amma wajibi ne ya rama azumin da ya sha din.
742: Shin kirkiro tafiya da gangan cikin watan Ramalana don guje wa yin azumi yana halalta?
A:Babu wata matsala cikin yin tafiya cikin watan Ramalana ko da kuwa don guje wa yin azumi ne. Wajibi ne ya sha ruwa.
743: Mutumin da yake da azumin wajibi a kansa sai ya kuduri aniyar rama azumin, to amma sai wani abu ya bijiro masa da zai hana yin azumin, kamar tafiya ta same shi bayan ketowar alfijir inda ya yi tafiyar to amma bai dawo ba sai bayan azahar kana bai aikata komai daga cikin abubuwan da suke karya azumi ba, sai dai kawai lokacin yin niyyar azumin wajibi ya wuce masa, kuma wannan ranar tana daga cikin ranakun da yin azumi mustahabi ne a cikinsu, to shin ya inganta ya yi niyyar azumin mustahabi?
A: Idan dai har yana da azumin wajibi a kansa to azumin mustahabi ba ya inganta a gare shi ko da kuwa bayan wucewar lokacin yin niyyar azumin wajibi ne.
744: Ni dai mutum ne da shan taba sigari ya kama ni sosai, a lokacin watan Ramalana ma dukkanin kokarin da na yi wajen kaurace wa tabar ya ci tura hakan kuwa ya kan sanya iyalaina cikin damuwa da bacin rai ni ma kuma na kan wahala da irin wannan yanayi da nake ciki. To mene ne hukumcina?
A: Azumin watan Ramalana dai a gare ka wajibi ne, sannan kuma bisa ihtiyati na wajibi ba ya halalta ka sha taba sigari alhali kana azumi. Haka nan kuma bai kamata ka cutar da wani ba tare da wani dalili ba.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved