XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
Muhimmaci Da Kuma Sharuddan Sallah

Ali Khamenei4

T338: Mene ne hukuncin mai barin salla da gangan ko kuma wasa da ita?

A: Sallolin nan na wajibi guda biyar da ake yinsu a kowace rana suna daga cikin muhimman wajibai a shari'ar Musulunci kai su ne ma ginshikin addini. Don haka barinsu ko kuma wasa da su haramun ne wanda ke sa mutum ya cancanci azaba.
T:339: Shin salla tana wajaba ga wanda ya rasa abubuwan tsarkin nan guda biyu (ruwa da kasa), wato ba shi da ruwa ko kuma abin da ya halalta a yi taimama kansa?
A: A bisa lhtiyat zai yi salla cikin lokaci, to amma daga baya ya rama ta tare da alwala ko kuma taimama.
T340: A bisa fatawarka, a wasu halaye ne ya halatta a yi "udul" (wato canza niyyar salla daga sallar da kake cikinta zuwa ga wata sallar) a cikin salla da ta zan wajiba?

A: Yin "udul" yana wajaba ne cikin halayen da za a kawo su a kasa:
1- Yin sa daga sallar la'asar zuwa azahar wato idan mutum yana sallar la'asar sai ya tuna cewa bai yi sallar azahar ba.
2- Daga sallar lisha zuwa magariba idan har ya tuna yayin da yake sallar lishar cewa bai yi magariba ba kana kuma bai wuce wajen yin "udul" din ba.
3- Idan yana da ramakon salloli guda biyu wadanda suke a jere sai ya manta har ya fara da ta biyun kafin ta farkon.
Sannan mustahabi ne yin "udul" a wasu wurare Daga cikinsu akwai:
1- Yin uduli daga sallar da ake yin ta cikin lokacinta zuwa ga ramako na wajibi, hakan kuwa mustahabbi ne idan har lokacin falalar ita wannan salla da ake lokacinta ba zai tsere ba.
2- Kana kuma yin uduli daga sallar wajibi zuwa ga ta mustahabi domin samun daman yin ta (wato wajibar) tare da liman.
3- Yin uduli daga sallar farilla zuwa ga nafila yayin sallar azahar din ranar juma'a ga wanda ya mance karanta suratul Juma'ati maimakon haka sai ya karanta wata sura ta daban har ya kai tsakiyarta ko ma ya wuce hakan, to mustahabi ne ya canza wannan farilla zuwa ga nafila don ya sake sallar farillar da suratul Juma'ati.
T342: Idan har jini ya ci gaba da zubowa daga hanci ko bakin mutum tun daga farkon lokacin salla har kusa da karshen lokacinta, to mene ne hukuncin salla a nan?

A: Idan har ba zai iya tsarkake jikinsa ba kana kuma yana tsoron fitar lokacin sallar to sai ya yi salla a cikin wannan yanayin.
T343: Yayin zikirorin mustahabi na cikin sallolin farilla, shin daidaita jiki da kuma rashin motsa wajibi ne?

A: Al'amarin daidaita jiki da kuma nitsuwa yayin salla ba shi da wani bambanci shin cikin zikirori na wajibi ne ko kuma na mustahabi. Na'am fadin zikiri da nufin zikirin alhali jiki na motsi babu laifi cikin hakan.
T344: A wasu lokuta a kan sa wa mara lafiya wata roba don fitan fitsari saboda rashin lafiyar da yake damunsa, a irin wannan yanayi fitsari zai dinga fito masa ko ba da sonsa ba, ko yana barci ko idonsa biyu, ko da kuwa yana salla ne, to a irin wannan yanayi shin wajibi ne ya sake salla ko kuma wannan sallar da ya yi ta wadatar?

A: Idan har yayi salla a cikin irin wannan hali dai-dai da yadda shari'a ta wajabta masa, to sallarsa ta yi, ba wajibi ba ne ya sake ko kuma ya rama ta ba.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din