BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
Hukumce-Hukumcen Salla- Lokutan Sallah
T345: Mene ne dalilin mazhabar Shi'a dangane da lokutan salla na ranaku? Kamar yadda ka sani ne ‘yan Ahlussunna daga lokacin da lokacin sallar lisha ya shiga to suna daukan sallar magariba a matsayin ramuko ne, haka nan lokacin azahar da la'asar ma. Saboda haka sun yi amanna da cewa yayin da lokacin lisha ya shigo sannan kuma liman ya tashi don yin sallar, to mamu ba za su iya yin sallar magariba tare da shi ba, wato su kawo sallar magariba da lisha lokaci guda ba.
A: Dalilin ‘yan Shi'a ya ginu ne bisa ayoyin Alkur'ani mai girma da hadisan Ma'aiki masu tsarki da kuma ruwayoyin da suka yi magana kan halalcin hada salloli biyu. A wajen ‘yan Sunna ma akwai ruwayoyin da suke nuni da halalci hada salloli biyu lokacin daya daga cikin biyun.
T346: Bisa la'akari da cewa karshen lokacin sallar la'asar shi ne gurub, kana kuma karshen lokacin sallar azahar shi ne kafin magriba da gwargwadon lokacin da sallar la'asar ta ke bukata, to tambaya a nan ita ce: Mene ne ake nufi da gurub ko magariba, shin shi ne faduwar rana ko kuma yayin da ake kiran sallar magriba (gwargwadon yanayin gurin da mutum yake)?
A: Karshen lokacin sallar la'asar shi ne faduwar rana.
T347: Mintuna nawa ne tsakanin faduwar rana da lokacin kiran sallar magariba?
A: To hakan ya bambanta ne gwargwadon yanayin da ake ciki a shekara.
T348: Na kan tashi a aiki ne bayan kurewar lokaci ta yadda na kan iso gida misalin karfe sha dayan dare ne, sannan kuma a lokacin aiki ba na samun damar yin sallar magariba da lisha saboda yawan masu shiga da fice (yawan aiki). Shin yin salla bayan sha dayan dare ya inganta.
A: Matukar ba ka wuce tsakiyan dare ba, babu laifi, sai dai yana da kyau ka yi kokarin ka ga ka yi sallar kafin karfe sha dayan daren, kai idan ma mai yiyuwa ne ka yi kokarin ganin ka yi sallar a farko-farkon lokacinta.
T349: Mene ne gwargwadon abin da idan mutum ya aikata za'a iya cewa ya riski salla a cikin lokacinta? Kana niyyarsa ta yin sallar a cikin lokacinta ta inganta. Kana kuma mene ne hukunci yayin da mutum ya ke shakkan shin wannan gwargwadon ya yi shi ne a cikin lokacin ko kuma?
A: Gwargwadon ra'aka guda cikin karshen lokaci yana wadatarwa a ce an yi salla a cikin lokaci, to amma idan kana kokwanto cewa lokacin da ya saura zai ishe ka yin raka'a guda a cikin lokaci ko a a, to a nan sai kawai ka yi niyyar saukar da abin da ke kanka ba tare da ka yi niyyar yin ta a cikin lokaci ko kuma ramako ba.
T351: Shin mene ne fatawarka kan lamarin alfijir din gaskiya (Fajr al-Sadiq) da kuma na karya (fajr al-kazib)? Kana kuma mene ne ya wajaba kan mai salla dangane da wannan al'amari?
A: Abin lura dangane da lokacin salla ko kuma azumi shi ne alfijir din gaskiya, gano hakan kuma yana wuyan mutum ne.
T353: Shin wajibi ne raba sallar azahar da La'asar wato a yi sallar azahar bayan shigan lokacinta kana kuma sallar la'asar bayan shigan lokacinta sannan kuma magriba da isha ma haka?
A: Bayan shigan lokaci mutum yana da zabi ko ya hada su ko kuma ya rarraba su.
T356: Ahlus-Sunna su kan yi sallar magariba gabannin ainihin faduwar ranar da shari'a ta tanadar, to shin yana halatta a gare mu lokacin aikin hajji da kuma sauran lokuta mu bi su salla ba tare da mun sake ta ba?
A: Ba tabbataccen al'amari ba ne cewa suna yin salla gabannin lokaci, sannan kuma bin su salla ba wata matsala a cikinsa kuma ya wadatar, to amma dai shigan lokaci al'amari ne da ba makawa sai da shi, sai dai in shi ma lokaci wuri ne na yin takiyya.
T357: Isar hasken zuwa kasa (duniya) ya kan dauki kimanin mintoci bakwai. To shin abin lura dangane da karshen lokacin sallar asuba shi ne fitowar rana ko kuma fitan haskenta zuwa ga duniya?
A: Abin lura shi ne fitowar rana da kuma ganin ta a gurin da mutum yake.
T359: A wasu lokuta kafafen watsa labarai sukan sanar da lokutan salla na kowace rana tun daga ranar da ta gabace ta, to shin ya halatta a dogara ga hakan da kuma irin kiran sallar da ake sa wa a gidajen Radiyo da talebijin wajen shigan lokaci?
A: Abin lura kawai a nan shi ne mutum ya sami nitsuwar kan cewa lokaci ya shiga, idan har ya samu ya samu hakan ta wannan hanya da aka ambata, to ba laifi ya dogara da su.
T360: Shin lokacin salla ya kan fara ne daga mujarradin fara kiran salla? Ko kuma wajibi ne a hakura har sai an gama kiran sallar daga nan sai a fara sallar? Sannan kuma shin ya halalta mai azumi ya fara shan ruwa daga lokacin da aka fara kiran salla ko kuma wajibi ne ya hakura har sai an gama kiran sallan?
A: Idan har mutum yana da yakinin cewa an fara kiran sallan ne bayan da lokaci ya shiga, to yin hakuri har zuwa a gama (kiran sallan) ba wajibi ba ne.
T361: Shin sallar mutumin da ya gabatar da salla ta biyu a kan ta farko, misali ya gabatar da sallar lisha kan magariba, ta inganta?
A: Idan har bisa kuskure ne ko kuma gafala ne ya gabatar da salla ta biyu, sannan sai bayan ya idar da sallar ya fahimci hakan, to sallarsa ta inganta. To amma idan har da gangan ya yi hakan, to ta baci.
T364: Mutumin da yana cikin sallar la'asar sai ya fahimci cewa bai yi sallar azahar ba, mene ne hukumcinsa?
A: Idan har yana tunanin cewa ya yi sallar azahar ne don haka sai ya fara sallar la'asar, to a lokacin da yake sallar la'asar din sai ya fahimci cewa lalle bai yi sallar azahar ba. To idan har yana cikin lokacin da sallolin biyu (azahar da la'asar) suka yi tarayya ne, to ba tare da bata lokaci ba sai ya sauya niyyarsa zuwa ga sallar azahar ya karasa sallar daga baya kuma sai ya yi sallar la'asar. Idan kuma hakan (wato fahimtar cewa bai yi sallar azahar din ba) ya faru ne a kebantaccen lokacin azahar, to bisa ihtiyati na wajibi sai ya koma zuwa ga sallar azahar ya cika sallar sannan daga baya kuma sai ya yi sallar azahar da la'asar a jeer, haka lamarin yake dangane da sallar magariba da lisha..
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved