T366: Idan har sakamakon tsananin rikici ko yaki ya sanya mutum ba zai iya ayyana inda alkibla take ba, to shin yin salla ta kowace jiha ya inganta?
A: Matukar dai babu wata jiha guda da hankalinsa ya fi kwanciya sannan kuma akwai lokaci, to bisa ihtiyati wajibi ne ya yi salla ta dukkanin jihohin hudu. To amma idan babu lokaci, to gwargwadon yadda yake da lokaci sai kalli jihar da yafi tsammanin nan ne alkibla din, ya yi salla.
T368: Idan mutum yana cikin yanayin da bai san ina ne alkibla ba, sannan kuma babu inda hankalinsa ya fi kwanciya da cewa nan ne alkibla, to mene ne ya hau kan mutum dangane da batun salla, wato ta wata jiha zai yi salla?
A: Dangane da wannan tambaya, bisa ihtiyati wajibi ya yi sallaci dukkanin jihohi hudun, idan kuwa babu lokacin da zai yi salla har sau hudu, to sai ya yi sallar gwargwadon yadda lokaci zai ba shi dama.