T370: Shin zama ko yin salla ko kuma wucewa a wuraren da hukuma azzaluma ta kwace daga wajen masu shi ba tare da yardansu ba ya halatta?
A: Idan har mutum yana da masaniya kan kwacen to hukuncinsa yana daidai da hukuncin kwace ba ya halatta a yi amfani da shi wajen salla da sauransu.
T372: Ni na kasance ina limancin salla a wasu makarantu, alhali kuma wasu bangare na wadannan makarantu an kwace su ne daga masu shi ba tare da yardansu ba, to shin mene ne hukuncin sallata da kuma sallar sauran dalibai a irin wadannan makarantu.
A: Idan har an ba da kwararan hujjoji sannan kuma jami'an da abin ya shafa suna da izini na doka wanda shari'a ta yarda da shi wajen gina wadannan makarantu, to yin salla a wajen babu matsala.
T373: Mutum ne ya dauki lokaci yana salla a kan darduma ko kuma da tufafin da khumusi ya hau kansa, mene ne hukumcin sallar tasa?
A: Matukar dai ya jahilci wajabtar khumusi kan wannan dukiya ko kuma hukumcin yin amfani da wadannan abubuwa, to sallolin da ya zuwa wannan lokacin ya yi sun inganta.
T374: Mutum ne yake zaune a gidan gwamnati, to sai aka umurce shi da ya bar gurin bayan cikan kwanakin da aka yarda masa ya zauna, to mene ne hukuncin salla da kuma azuminsa a wannan gidan bayan wannan lokaci?
A: Idan har ba an yarda masa ya ci gaba da zama a gidan ba ne bayan cikan kwanakin, to amfanin da zai yi da gidan yana matsayin kwace ne.
T377: Shin akwai karhanci ne cikin salla a kan dardumar da aka yi zane a jikinta ko kuma a kan turbar da a jikinta a ka yi zane?
A: A kan kansa babu matsala, to sai idan har hakan zai zamanto makami a hannun masu adawa da Shi'anci wajen tuhumar ‘yan Shi'a, to yin (wannan darduma) da yin salla a kanta ba ya halalta. Sannan kuma akwai karhanci cikin hakan matukar dai zai dauke hankalin mai sallar.
T378: Idan wurin da mutum zai yi salla a wajen ba shi da tsarki amma wajen da zai yi sujada yana da tsari, shin sallarsa ta inganta?
A: Matukar dai najasar dake wajen sallar ba za ta shafi tufafi ko jikinsa ba kuma wajen da zai yi sujada yana da tsarki, babu wata matsala cikin yin salla a wajen.
T384: Idan da mutum zai yi salla a gurin kwace to amma akan darduma ko tabarma da makamancinsu to shin sallarsa ta inganta ko kuma?
A: Salla a wajen kwace ba ta inganta ko da kuwa a kan darduma ce ko tabarma da aka shimfida a wajen.
T387: Shin salla a gurin da aka sanya haramtacciyar kida ta inganta ko kuma?
A: Yin salla a wannan wuri idan ya jawo sauraron kida na haram to bai halatta a zauna a gurin ba, sai dai kuma sallarsa ta inganta, idan kuma kidan zai hana mutum samun fadaka da mai da hankali, to yin salla a gurin makaruhi ne.