Teya Salat
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Masallaci

Ali Khamenei4

T389: Bisa la'akari da cewa mustahabi ne mutum ya yi salla a masallacin unguwarsu, to shin akwai matsala cikin barin masallacin unguwar da tafiya babban masallacin garin don yin sallar jam'i a can?

A: Idan har barin masallacin unguwarsu da nufin tafiya wani masallaci na daban don sallar jami'i ne musamman babban masallacin garin to babu matsala.
T391: Shin sallar mata a gida ne ya fi ko kuma a masallaci?

A: Falalar yin salla a masallaci ba ta takaita ga maza kawai ba.
T400: Wani lokaci ne ya ke halalta a yi amfani da ‘loud speaker' masallaci wanda muryarsa take fita wajen masallacin? Sannan kuma mene ne hukumcin watsa wakokin juyin juya hali ko karatun Alkur'ani kafin kiran salla?

A: Watsa karatun Alkur'ani na ‘yan wasu mintoci kafin kiran salla matukar ba zai cutar da makwabta ko kuma mutanen unguwar ba, babu matsala.
T403: A kokarin da ake yi na fadada wata hanya, wadansu masallatai sun fado kan titin da ya zama wajibi ne a rusa wadansu masallatan dukkansu, wadansu kuma wasu bangarensu ne za a rusa don ba wa motocin da suke aiki daman wuce cikin sauki. Don Allah mene ne ra'ayinku kan hakan.

A: Rusa dukkan masallaci ko kuma wani sashi nasa ba ya halalta, sai dai idan akwai maslaha cikin hakan kuma ba zai iya rufe ido kan hakan ba.
T419: Shin ya halalta wadanda ba musulmi ba su shiga masallaci, koda kuwa don ganin ababen tarihi ne?

A: Shigarsu Masjid al-Haram haramun, a sauran masallatai idan har hakan zai kasance cin mutumci da keta hurumin masallacin ne, ba ya halalta, kai bai kamata su shiga masallaci ba.
T420: Shin salla a masallacin da kafirai ne suka gina shi yana halatta?

A: Ba wata matsala ga sallar da aka yi a cikin irin wannan masallaci.
T421: Shin ana iya karban taimakon da kafiri ya bayar wajen gina masallaci?

A: Ba wata matsala ga hakan.
T422: Idan mutum ya yi mafarki a cikin masallaci cikin dare, to idan ba zai iya fita daga masallacin ba yayin da ya farka, to mene ne zai yi?

A: Idan har ba zai iya fita daga masallacin zuwa wani guri ba, to wajibi ne ya gaggauta yin taimama don ta halatta masa zama a cikin masallacin.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din