XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Tufafin Mai Salla

Ali Khamenei4

T428: Shin salla da tufafin da nake shakkun najastuwansu tana inganta?

A: Duk tufafin da ake da shakka kan najastuwarsu to ana daukarsu masu tsarki ne kana kuma salla da su tana inganta.
T429: Shin akwai matsala ta shari'a cikin yin salla da belt din da na sayo shi daga kasar Jamus (ko wata kasa wacce ba ta musulmi ba) sannan kuma ina shakka kan cewa fatar da aka yi shi da shi na dabi'a ce ko kuma wacce aka sana'anta ne ko kuma na dabbar da aka yanka ta hanyar da shari'a ta tanadar ne ko kuma a'a? Sannan mene ne hukumcin sallolin da na yi su da shi?

A: Idan har ana shakkan cewa shin fatar ta dabi'a ce ko kuma wacce aka sana'anta ne, to babu matsala cikin sallar. Sai dai idan har bayan an tabbatar da cewa fata ce ta dabi'a amma ana shakkun kan an yanka dabbar yadda shari'a ta tanadar ne ko kuma a'a, to a nan ba najasa ba ne sai dai ba ya halalta a yi salla da shi. Sallolin da aka yi da shi alhali an jahilci hukumcinsa, ba sai an rama ba.
T430: Idan har mai salla yana da tabbacin rashin najasa a jikinsa ko tufafinsa, sai ya yi salla, to bayan hakan sai ta bayyana masa cewa jikinsa ko tufafinsa suna da najasa, shin sallarsa ta baci ko kuma? Kana kuma da ace zai gano hakan a tsakiyar sallar tasa, yaya zai yi?

A: Idan har bai san da kasantuwar najasar ba sai bayan da ya idar da sallar, to sallarsa ta inganta ba wajibi ba ne ya sake sallar ko kuma ya rama to amma idan ya gano hakan yayin da yake cikin salla, idan har zai iya kawar da najasar ko kuma cire tufafin ba tare da ya aikata wani abin da zai bata masa salla ba, to wajibi ne ya yi hakan kana ya cika sallarsa. Idan kuwa ba zai iya kawar da najasar ko kuma cire tufafin tare da kiyaye yanayin sallar ba, kuma ya san akwai yalwataccen lokaci to a nan wajibi ne ya yanke sallar, kana ya sake ta bayan ya gusar da najasar ko kuma ya sake tufafin.

T432: Mace ce ta ga gashinta ya fito fili yayin da take salla, sai ta yi maza- maza ta rufe shi, shin wajibi ne ta sake sallar?
A: Matukar dai fitan gashin ba da gangan ba ne, sake salla ba wajibi ba ne a kanta.
T433: Mutumin da lalura ta tilasta masa tsarkake wajen fitan fitsarinsa da dutse ko ice ko kuma wani abu na daban, sannan bayan dawowarsa gida ya yi tsarki da ruwa. To shin yayin da yake son yin salla wajibi ne sai ya sake wandonsa (pant) dake ciki ko kuma ya tsarkake shi?

A: Matukar dai tufafin nasa bai najastu da danshin fitsarin ba, to tsarkake tufafin ba wajibi ba ne.
T435: Da ace mutum zai rike hankici da makamantansa wanda ya najastu da jinni ko kuma ya sanya shi a cikin aljihunsa yayin da yake salla, shin sallarsa tana inganta?

A: Idan har hankicin karami ne ta yadda ba za a iya rufe al'aura da shi ba, to babu wata matsala.
T436: Shin salla da tufafin da aka sanya masa turaren da akwai alkohol a cikinsa tana inganta?

A: Ba laifi a yi salla da shi idan har najasar wannan turare bai tabbata masa ba.
T437: Shin ina ne ya zama wajibi ga mace ta rufe shi yayin salla, shin akwai matsala a sanya guntayen tufafi (tufafi mai guntun hannu) da kuma rashin sanya safa?

A: Abin da ake lura da shi shi ne kasantuwan tufafin ya rufe dukkan jiki ban da fuska (gwargwadon inda ake wankewa yayin alwala), kana ban da tafukan hannu kuma ban da kafafu zuwa idon kafa. Idan kuma akwai muharraminta a wajen to wajibi ne ta rufe kafafun nata.
T441: Shin kasantuwan gashi ko kuma yawun kyanwa a jikin tufan mai salla yana bata salla?

A: Na'am yana bata salla.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din