Old school Easter eggs.
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Kaskantar Da Kai

Ali Khamenei2

Manzon Allah (s.a.w.a) ya
ce:-.
ﻭﺟﺎﺀﻩ ﺭﺟﻞ ﺑﻠﺒﻦ ﻭﻋﺴﻞ ﻟﻴﺸﺮﺑﻪ
ﻓﻘﺎﻝ (ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ )
ﺷﺮﺍﺑـﺎﻥ ﻳﻜﺘﻔﻰ ﺑﺄﺣﺪﻫﻤﺎ ﻋﻦ
ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻻ ﺃﺷﺮﺑﻪ ﻭﻻ ﺃﺣﺮﻣﻪ
ﻭﻟﻜﻨﻲ ﺃﺗﻮﺍﺿﻊ ﻟﻠﻪ ﻓﺈﻧﻪ ﻣﻦ
ﺗﻮﺍﺿﻊ ﻟﻠﻪ ﺭﻓﻌﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻦ ﺗﻜﺒﺮ
ﻭﺿﻌﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻦ ﺍﻗﺘﺼﺪ ﻓﻲ
ﻣﻌﻴﺸﺘﻪ ﺭﺯﻗﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻦ ﺑﺬﺭ
ﺣﺮﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻠﻪ
ﺁﺟﺮﻩ ﺍﻟﻠﻪ
"Wani mutum ya zo wa
(Manzon Allah) da madara
da zuma domin ya sha, sai
Manzon Allah (s.a.w.a) yace
abubuwan sha biyu,
dayansu yana wadatar da
daya. Don haka ba zan sha
su tare ba, amma ba zan
haramta ba, sai dai ni ina
mai kaskantar da kai na ga
Allah. Saboda duk wanda ya
kaskantar da kansa ga Allah,
Allah zai daukaka shi.
Wanda kuma yayi girman
kai, Allah zai kaskanta shi.
Duk wanda kuma yayi tattali
a rayuwarsa, to, Allah zai
azurta shi. Wanda kuma
yayi almubazzaranci, to,
Allah zai kuntata masa.
Kuma duk wanda ya
yawaita ambaton Allah,
Allah zai ba shi kyakkyawan
sakamako".
(Tuhaful-Ukul shafi na 46).
*****
Akwai yiyuwar wasu su
tsammaci cewa idan
Ma'asumi (a.s) (wanda Allah
ya tsarkake shi) ya kaurace
wa wasu daga cikin
ni'imomin Allah hakan yana
nufin ya haramta su ke nan,
don haka ne Manzon Allah
(s.a.w.a) ya bayyana cewa
ba zan yi amfani da su ba
tare, amma ba zan haramta
wa mai son yin amfani da
su tare ba. Domin ba na son
yin amfani da dukkanin
ni'imomin da aka halatta
mini. Dangane da ma'anar
daukakar da Allah zai yi wa
mutumin (da ya kaskantar
da kai ga Allah) kuwa yana
nufin daukakan matsayi ne
na ma'anawiyya, sai dai
akwai yiyuwar ya zame
daukaka na zahiri ma,
amma abin da yake a fili
kuma tabbas shi ne
daukaka ce ta ma'anawiyya
da ruhi. Wato duk wanda ya
kaskantar da kai ga Allah,
to, Allah madaukakin Sarki
zai daukaka kyawawan
dabi'unsa da ruhinsa kuma
ya azurta shi da karamomi
madaukaka. Haka nan abin
da ake nufi da kaskantarwa
shi ne Allah ya kaskantar da
matsayin mutum na ruhi,
duk da cewa akwai yiyuwar
kaskantarwar ta zamanto ta
zamantakewa wato mutum
ya zama kaskantacce a
tsakanin al'umma, maras
matsayi.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din