Teya Salat
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Karatu Da Hukumce-Hukumcensa

Ali khamenei

T458: Mene ne hukumcin sallar da a bayyana karatunta a fili ba?

A: Wajibi ne maza su bayyana karatun Fatima da Sura a sallolin asubahi, magariba da lisha (raka'oi biyu na farkonsu). Idan har bisa mantuwa ko jahilci sai mutum ya karanta su a boye, to sallarsu ta yi, amma idan da gangan suka yi hakan to sallarsu ta baci.
T459: Idan mutum yana son rama sallar asubahi, to shin zai yi karatunta a bayyane ne ko kuma a boye?

A: Wajibi ne a karanta Fatiha da Sura a sallolin asubahi da magariba da lisha a bayyane ko a cikin lokacinsu ne ko kuma yayin ramuwarsu ko da kuwa ramuwarsu da rana ne. Idan kuwa mutum da gangan ya ki bayyanawa to sallarsa ta baci.
T460: Mun san cewa raka'a guda ta salla ta kumshi niyya, kabbarar harama, fatiha, sura, ruku'u da sujada ne. Sannan a bangare guda kuma a sallar azahar da la'asar da raka'a ta uku ta sallar magariba da kuma raka'oi na uku da hudu na sallar magariba ana yin su ne a boye. To amma a sallar jam'in da ake sanyawa a gidan talabijin kai tsaye mu kan ga limamin da ke jagorancin sallar ya kan yi zikirin da ake yi cikin ruku'u da sujada a raka'a ta uku a bayyane ne. To bisa la'akari da cewa ruku'u da sujadan wasu juzu'i ne na raka'oin da wajibi ne a karanta su a boye. To mene ne hukumcin hakan?

A: Wajibcin bayyana karatu a sallolin magariba da lisha da asuba da kuma wajibcin boye karatu a sallolin azahar da la'asar ya kebanci karatun fatiha da sura ne. kamar yadda wajibcin boye karatu a raka'oin da ba biyun farko na sallolin magariba da lisha ya kebanta ne kawai da karatun fatiha ko kuma tasbihohin da ake yi ne a raka'a ta uku ko ta hudu. Amma dangane da zikirin da ake yi a ruku'u ko sujada da kuma tahiya da sallama da sauran zikirorin wajibi da ake yi cikin salla, mutum yana da zabin ko dai yayi su a bayyane ko kuma a boye.
T461: Idan mutum yana so, baya ga raka'oi sha bakwai na sallolin wajibi na ranaku, yana son ya sake yin wasu raka'oi sha bakwai a matsayin sallolin ramuko ko kuma saboda ihtiyati. To shin zai yi karatun raka'oin farko da na biyu na sallolin asubahi da magariba da lisha a bayyane ne ko kuma a boye.

A: Dangane da batun bayyana karatu ko boyewa cikin sallolin wajibi babu wani bambanci tsakanin yin sallar a lokacinta da kuma ramuko, ko da kuwa ita wannan sallar da za a yi din ta ihtiyati ce.
T466: Mutum ne tun farko ma ko kuma bisa al'adarsa yana da niyyar karanta fatiha da suratu Ikhlas ne, to bayan ya karanta bismillah sai ya mance bai ayyana surar da zai karanta ba. To shin wajibi ne tun farko sai ya ayyana wata sura kafin ya karanto bismillah?

A; Sake karanta Bismillah ba wajibi ba ne, face dai yana iya ci gaba da karanta kowace sura da wannan bismillan.
T468: Shin mutum yana iya karatun salla a cikin zuciyarsa ba tare da fitar da lafuza ba?

A: Hakan ba ya wadatarwa, dole ne a fitar da lafuzan.
T469: Kamar yadda wasu malamai suka bayyana cewa wasu daga cikin surorin Alkur'ani kamar suratul Fil da Kuraish, da kuma Suratul lnshirah da suratu Duha sura guda, wato idan mutum ya karanta misali suratul Fil to wajibi ne ya zo da suratu Kuraish, ko kuma idan ya karanta suratu Duha to wajibi ne ya zo da Alam Nashraha, to da ace mutum zai karanta suratul Fil ita kadai, ko kuma Alam Nashraha ita kadai, tare da rashin sanin hukuncin, to mene ne hukuncinsa?

A: Idan har bai nuna gazawa ba wajen neman ilimin hukumcin to sallarsa ta inganta.
T470: Idan mutun ya mance yayin da yake salla misali a raka'a ta uku ta sallar azahar ya karanta fatiha da sura, kana bai gano hakan ba sai bayan ya idar da sallarsa, to shin wajibi ne ya sake ta? kana kuma idan ma bai gano hakan ba, gaba daya shin sallarsa ta inganta?

A: A irin wannan yanayi sallarsa ta inganta.
T471: Shin mata za su iya karanta fatiha da sura na cikin sallolin asubahi da magariba da lisha a bayyane?

A: Na'am za su iya karatunsu a bayyane ko kuma a boye, to amma idan har wani wanda ba muharraminsu ba zai ji su, to yana da kyau su yi karatun a boye.
T475: Shin wajibi ne a salla a karanta sura cikakkiya bayan Fatiha, ko kuma wani sashi na surar ya wadatar? A yanayi na farko shin yana halatta bayan karanta sura cikakkiya mutum ya sake karanta wasu ayoyi na Alkur'ani?

A: A sallolin farilla na rana karanta wasu ayoyin na Alkur'ani maimakon sura cikakkiya ba ta wadatarwa, to amma karanta wasu ayoyin na Alkur'ani da nufin Alkur'ani bayan sura cikakkiya babu wata matsala ga hakan.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din