Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
Hukumce-Hukumcen Zikirin Cikin Sallah

Ali Khamenei4

T480: Shin akwai wata matsala cikin karanta zikirin sujada a wajen ruku'u da karanta zikirin ruku'u a wajen sujada da gangan?
A: Matukar dai an yi hakan ne da nufin ambato (zikirin) Allah Madaukakin Sarki, babu matsala cikin hakan, kuma ruku'u da sujadarsa sun inganta.
T481: Idan mutum bisa kuskure ya karanta zikirin ruku'u yayin sujada sannan a daya bangaren kuma akasin hakan wato ya karanta zikirin sujada yayin ruku'u, sai daga baya ya fahimci kuskurensa ya gyara kuskuren nasa, shin sallarsa ta baci?

A: Babu matsala cikin hakan kuma sallarsa ta inganta.
T482: Idan mai salla yayin da yake cikin sallar ko kuma bayan idar da sallar ya fahimci cewa ya yi kuskure wajen karanta zikirin ruku'u ko sujada, mene ne hukumcinsa?

A: Matukar bayan ruku'u ko sujadan ne ya tuna (ya fahimci hakan) to babu wani abin da ya hau kansa.
T483: Shin fadin tasbihat al-arba' (wato subhanallah, walhamdu lillahi, wa la'ilaha illallah, wallahu akbar) sau daya a raka'a ta uku da ta hudu ya wadatar?

A: Ya wadatar, duk kuwa da cewa ihtiyati shi ne a karanta sau uku.
T484: Kamar yadda aka sani adadin tasbihat al-Arba' da ake karantawa cikin salla uku ne, to amma bisa kuskure sai mutum ya karanta ta sau hudu. Shin Allah Ya karbi sallarsa?

A: Babu matsala cikin hakan.
T485: Mutum ne bai san adadin tasbihat al-arba' da ake karantawa a raka'oi na uku da hudu ba, shin sau uku ne ake yi ko kuma sama da haka ko kasa da haka, to mene ne hukumcinsa?

A: Sau guda ma tana wadatarwa, kuma babu wani abin da ya hau kansa. Sannan kuma matukar bai tafi zuwa ruku'u ba yana iya gina abin da ya karanta bisa mafi karanci sai ya cika har ya samu yakinin cewa ya karanta sau uku.
T487: Me ake nufi da zikiri? Shin haka ya hada da salati Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da mutanen gidansa?

A: Duk wata kalma (ko jumla) da ta kumshi ambaton Allah Madaukakin Sarki, ana kirga ta cikin zikiri (ambaton Allah), salati ga Annabi da Alayensa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) kuwa yana daga cikin mafi girma da kyaun zikirori.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


The Soda Pop