T489: Mene ne hukuncin sujada ko taimama a kan siminti?
A: Sujada da taimama a kan wadannan abubuwa guda biyu babu matsala cikinsu. Duk kuwa da cewa bisa ihtiyati an so a nesanci yin taimama a kan siminti.
T490: Shin akwai matsala cikin yin sujada kan turbar da ta yi baki sannan kuma ta yi dauda ta yadda daudar da ta yi tsananin da ta kan hana haduwa fatar goshi da asalin turbar ?
A: Matukar dai wannan daudar ta kasance ta yadda ta zama wata garkuwa da take hana haduwar fatar goshi da turbar, to sujada da kuma salla ba su inganta ba (sun baci).
T491: Macen da hijabinta ya rufe mata wajen yin sujada a kan turba musamman ma dai goshinta inda take yi sujada din, shin wajibi ne ta rama sallar da ta yi?
A: Matukar ba ta fahimci kasantuwar wannan garkuwa (da take hana saduwar fatar goshi da rubar ba) yayin da take yin sallar, to ramuwar sallar ba wajibi ba ne a gare ta.
T492: Mene ne hukumcin sallar macen da ta sanya goshinta kan turba yayin sujada, to amma sai ta fahimci cewa goshin nata gaba daya bai hau kan turbar ba saboda hijbai ko dan kwalin da take sanye da shi, don haka sai ta daga kanta don ta gyara sannan sai ta mayar da kan nata bayan ta gyara kan turbar? Idan har aka dauki wannan aiki nata (wato daya goshinta da kuma sake mayar da shi) a matsayin wata sujada mai cin gashin kanta, to mene ne hukumcin da ya hau kanta?
A: Wajibi ne maimakon ta daga goshin nata sama ta yi kokarin jan goshin nata a hankali ta koma da shi gaba daya kan turbar. Haka nan kuma matukar daga kan nata da ta yi daga kasa don ta sami damar yin sujada a kan turbar sakamakon jahilcin da take da shi ne ko kuma saboda mantuwa kawai cikin wata daga cikin raka'oin sallar, to sallar ta ta inganta, ba wajibi ba ne ta sake ramawa. To amma idan har hakan ta yi su ne da gangan ko kuma bisa ilimi ko kuma ya yi hakan cikin dukkan sujada guda biyu na raka'a guda, to sallarsa ta baci kuma rama wannan salla ta wajaba a kansa.
T:493: An bayyana cewar wajibi ne dukkanin gabobin nan bakwai su kasance a kasa yayin sujada, to amma ni saboda matsalar da nake da ita a jikina ba zan iya yin hakan ba, saboda ni ina amfani ne da irin keken guragun nan saboda raunin da na samu a lokacin yaki. Yadda nake yin sallar shi ne ko dai in dauki turbar ina sanya ta a kan goshina ko kuma in dora ta kan hannun keken da nake kai ina sujada a kanta. To shin hakan yana inganta ko kuma a'a?
A: Idan har ba za ka iya sanya turbar kan hannun kujerar keken naka ba ko kuma kan wani abu na daban kamar filo ko kuma kujera ka yi sujadar a kanta ba, to wajibi ne ka yi sujadar yadda ka ambata, kuma sallarka ta inganta. Idan kuwa ba haka ba to kana iya yin sallar duk yadda ta sawwaka maka ko da kuwa ta hanya sunkuyo da kuma ishara ne, ka yi sujada ruku'u, sallarka ta inganta. Ina rokon Allah da Ya ba ka dacewa.
T494: A halin yanzu ana yin wata irin turba da take nuni da adadin raka'a da kuma sujadar da mutum ya yi a rubuce don a rage irin shakkar da mutum ya ke fama da ita. To amma bisa la'akari da cewa a lokacin da mutum ya dora goshinsa kan wannan turbar saboda spring din da ke cikinta ta kan lotse kasa, to shin sujadar mutum ta inganta? Ina fatan za ka min Karin bayani kan ra'ayinka kan wannan lamari.
A: Matukar wajen da ake sanya goshi waje ne da aka yi shi da daya daga cikin abubuwan da suka halalta a yi sujada a kansu, to sujadarsa ta inganta sannan kuma bayan da ya sanya goshin nasa ya tsaya kyam ya daidaitu ba tare da wani motsi ba, to sujada kan wannan abu ba shi da wata matsala.
T494: Yayin zaman da ake bayan sujada wace kafa ce ake dora ta kan yar uwarta?
A: Mustahabi ne a sanya zahirin kafar dama a kan tafin kafar hagu.
T495: Mene ne ya wajaba mutum ya aikata yayin da ya ji an karanto ayoyin da ake musu sujada a cikin rediyo ko kuma ta hanyar rikoda?
A: Sauraren ayoyin sujada ta hanyar kaset ba ya wajabta sujada, to amma yayin da mutum ya saurare su ta hanyar rediyo ko kuma ta hanyar "lasafika" daga mai karatun kai tsaye, to wajibi ne, bisa ihtiyat, ya yi sujada.