Duck hunt
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
Abubuwan Da Suke Bata Sallah

Ali Khamenei4

T501: Shin ambaton tabbatar da wilaya ga Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cikin tashahhud (tahiya) yana bata salla?

A: Ka yi salla ciki kuwa har da tashahhud irin yadda manyan maraja'an shi'a (Allah ya kara yawansu) suka ambata cikin littafinsu na hukumce-hukumce kada ka kara wani abu a kai ko da kuwa kalmar gaskiya ce kuma abin da aka fadin ingantaccen abu ne.
T502: Yayin da mutum yake sallar jam'i tare da ‘yan'uwa ‘yan Ahlussunna, bayan da liman ya gama karanta Suratul Fatiha, su kan daga muryarsu gaba daya su ce ‘amin', mene ne hukumcin wannan aiki.

A: Idan mutum yana cikin yanayi ne na takiyya, to fadin ‘amin' din babu wata matsala cikinsa, to amma idan ba a irin wannan yanayi ba fadin hakan ba ya halalta.
T503: Idan mutum ya ga wani karamin yaro zai aikata wani abin da zai cutar da kansa alhali kuwa yana cikin salla, to shin ya halatta ya daga muryarsa yayin karatu ko zikiri don janyo hankalin yaron ko kuma wanda yake cikin gidan dan kawar da wannan abu? Kana kuma mene ne hukuncin yin ishara da hannu ko kuma gira don jawo hankalin wani mutum daban kan wani al'amari, ko kuma dan amsa wata tambayar da aka masa?

A: Idan har wannan daga sauti yayin karatu ko zikiri don jawo hankalin wani ba zai iya sauya yanayi da tsarin sallar ba, to babu wata matsala. Amma da sharadin cewa ya yi hakan ne da niyyar yin karatun ko kuma zikirin. Na' am magana yayin salla, ko kuma motsin da zai haifar da rashin nitsuwa, ko kuma ya kawar da yanayin salla to hakan yana bata salla.
T504: Idan mutum ya yi dariya yayin salla saboda tunawa da wani abin dariya, ko kuma don faruwar wani abin dariyan, shin hakan yana bata salla ko kuma?

A: Idan har dariyar tana da sauti - wato kyalkyalawa - to salla ta baci.
T505: Shin shafa fuska da tafin hannuwa bayan an gama kunutin salla yana salla. Idan har yana bata sallar, to ana daukan hakan a matsayin sabo da zunubi ne?

A: Akwai karhanci cikin hakan sai dai ba ya bata salla.
T506: Shin rufe ido yayin salla ya halatta domin a wasu lokuta barin idon a bude kan iya kawar da hankalin mutum daga sallar da sanya mutum cikin tunace-tunace?

A: Babu matsala ta shari' cikin hakan, ko da yake dai an karhanta yin hakan.
T507: Shin ci gaba da fada da kiyayya tsakanin mutane biyu har na tsawon kwanaki uku yana bata salla da azuminsu?

A: Fada da kiyayya tsakanin mutane biyu ba ya bata musu salla ko azuminsu, duk kuwa da cewa hakan abin kyama ne a shari'a.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din