T509: Mene ne ra'ayin (fatawar) mai girma dangane da amsa sallamar da ba a yi ta da sigar sallama (salamu alaikum) ba?
A: Idan har yayin salla ne to amsa irin wannan sallama ba ya halalta, amma idan har ba a lokacin salla ba ne sannan kuma kalma ce da mutane suke ganinta a matsayin sallama, to bisa ihtiyati ana iya amsawa.
T510: Shin amsa sallamar kananan yara (yaro da yarinya) wajibi ne?
A: Wajibi ne amsa sallamar kananan yara masu iya rarrabewa kamar yadda ya wajaba a amsa sallamar manyan mutane.
T511: Idan mutum ya ji an yi salla to saboda dalilin gafala ko kuma dai wani dalilin na daban sai bai amsa sallamar ba, to bayan wani lokaci ya tuna to shin amsa wannan sallamar wajibi ne.
A: Idan har tazarar ta kai ta yadda ba za a iya cewa ya amsa sallamar ko kuma gaisuwar ba, to ba wajibi ba ne.
T512: Da wani mutum zai yi sallama sama da sau daya a lokaci guda, ko kuma mutane da yawa suka yi sallama, to shin amsa sallama guda yana wadatarwa ga gaba dayansu?
A: Dangane da tambaya ta farko, amsa guda daya ta wadatar, a yanayi na biyu kuma amsa guda da sigar da za ta game dukkansu, da nufin amsa sallamarsu, ya wadatar.
T513: Mutum ne yayin sallama maimakon fadin ‘assalamu alaikum' sai ya yi amfani da kalmar ‘salam' to shin amsa sallamarsa wajibi ne?
A: Matukar a dabi'ar mutane ana daukan hakan a matsayin sallama, to amsa irin wannan sallama wajibi ne.