T514: Mene ne hukumcin mutumin da ya yi shakka cikin raka'arsa ta uku ta salla shin ya yi kunuti ko kuma a'a, shin zai cika sallarsa ne ko kuma zai yanke sallar ne daga lokacin da ya samu wannan shakkar?
A: Ba zai damu da wannan shakkar ba, sallarsa kuma ta inganta. A irin wannan yanayi babu wani abin da ya hau kan mukallafi.
T515: Shin a sallar nafila ana damuwa da shakkar da aka yi wanda ba ta shafi raka'oi ba misali shakka kan ko sujada daya mutum ya yi ko kuma biyu ko kuma a'a?
A: Hukumci shakka cikin maganganu da ayyukan sallar nafila daidai ya ke da na shakka cikin maganganu da ayyukan sallar farilla. Wato matukar mutum bai wuce muhallin wadannan ayyuka (da aka yi shakka cikinsu ba) ba to zai kula da su (wato zai aikata su). Idan kuwa har ya wuce muhallin, to ba zai damu da wannan shakkar ba.
T516: Ana cewa mai yawan shakka kada ya damu da shakkar tasa, to amma me zai yi yayin da shakkar ta zo masa yayin salla?
A: Abin da zai yi shi ne ya dauka cewa ya riga ya aikata aikin da yake shakkun a kansa, sai dai idan hakan ya zama wuri ne da zai haifar da bacin salla, to a wannan hali sai ya dauka cewa bai aikata shi ba, ba tare da wani bambanci ba tsakanin raka'oi da ayyuka da maganganun salla.
T517: Idan mutum ya gane cewa lbadunsa na shekaru ba daidai ya yi su ba, ko kuma ya yi shakkan hakan, to mene ne zai yi?
A: Ba'a lura da duk wata shakkar da aka yi ta bayan aiki, idan kuma har yana da yakinin bacin ayyukan nasa, to wajibi ne ya rama abin da za a iya riskarsa.
T520: Idan mutum bisa mantuwa ya sauya wasu ayyukan salla da wasunsu ko kuma a yayin sallar tasa idanuwansa suka kai ga wani wajen (da bai kamata ya gani ba) ko kuma yayi wata magana bisa kuskure, shin sallarsa ta baci? Sannan kuma wani hukumci ne ya hau kansa?
A: Aikin da aka yi shi cikin mantuwa yayin salla ba ya bata salla, sai dai a wasu wajajen hakan ya kan wajabta yin sujada ta rafkanwa sai dai kawai idan wani rukunin salla ne aka rage ko aka kara, to a nan kan salla ta kan baci.
T521: Da mutum zai mance wata raka'a ta salla kana sai a raka'ar karshe ya tuna. A matsayin misali, kamar idan ya zaci cewa raka'ar farko ta sallarsa a matsayin raka'a ta biyu sai ya zo da ta uku da ta hudu, to amma a raka' a ta karshe (wato ta hudun) sai ya fahinci ita ce ta uku, to me zai yi?
A: Wajibi ne gabannin sallama ya zo da raka'a gudar da ya mance kana sai ya yi sallama bayan haka, to a irin wannan yanayin da zai zo da kari a bisa rabkanuwa, ko kuma ya bar wasu wajibai wadanda ba rukuni ba ne, to wajibi ne ya zo da sujadar rabkanuwa. Da kuma zai bar tahiyar wajibi to wajibi ne a bisa lhtiyati ya rama ta.
T522: Idan mutum bisa kuskure ya karanta wata kalma cikin kalmomin zikirin salla ko kuma wata aya daga cikin ayoyin Alkur'ani ko kuma addu'a kunuti ba daidai ba, to shin sujadar rabkanwa ta wajaba a kansa?