Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Sallah Ramukon Sallah

Ali Khamenei4

T523: Ni dai har zuwa lokacin da na kai shekaru sha bakwai ban san wani abu dangane da batun yin mafarki da wanka da makamantansu ba, kuma ni ban ma taba jin wani abu dangane da su ba. Ban san ma'anar janaba da wajibcin wanka ba, don haka salloli na da azumi na suna da matsala. Ina fatan za ka min bayanin nauyin da ya hau kaina?

A: Wajibi ne ka rama dukkanin sallolin da ka yi su cikin janaba, to amma azumin da ka yi cikin janabar ba tare da kana da masaniya da asalin janabar ba sun inganta kuma sun wadatar. Ba ka da ramako a kanka.
T524: Mutumin da bai san ko akwai ramuwar salla a kansa ba ko kuma a'a, idan ya yi sallolin mustahabi da na nafiloli da nufin cewa idan har yana da sallar ramuko a kansa, to shin wadannan salloli sun wadatar masa kuma za a dauke su a matsayin ramako?

A: Ba za a lissafi sallolin mustahabi da nafiloli a matsayin sallolin ramuko ba. Idan har yana da sallolin ramako a kansa to wajibi ne ya yi sallar da niyyar ta ramako ne.
T525: Kimanin watanni shida kenan na kai shekarar balaga. Amma 'yan makonni kafin hakan na kasance ina tunanin cewa alama guda kawai ta balaga ita ce cika shekaru sha biyar (na hijira kamariyya). To amma yanzu na sami wani littafi da yake bayani kan alamomin balaga ta 'yan maza inda a cikinsa aka ambaci wasu alamu da siffofi wadanda na kasance ina da su amma dai ban san lokacin da suka bayyana min ba. To shin akwai ramuwar salla da azumi a kaina kenan ko kuma a'a? To bisa la'akari da cewa a wasu lokuta na kan yi salla sannan kuma a shekarar da ta wuce ma na azumci dukkanin watan, to mene ne nauyin da ke kaina?

A: Wajibi ne ka rama dukkanin salloli da azumin da kake da yakinin cewa sun kubuce maka bayan da ka kai shekarun balaga da kuma hawar nauyi na shari'a a kanka.
T526: Da mutum zai yi wankan janaba sau uku a cikin watan Ramalana misali a ranar ashirin da ranar ashirin da biyar da kuma ranar ashirin da bakwai to bayan hakan sai ta bayyana masa cewa É—aya daga cikin wadannan wanka ba daidai ya yi shi ba, to mene ne ya wajaba a kansa dangane da salla da azumi?

A: Azuminsa dai ya inganta, amma bisa ihtiyati wajibi ne ya sake salla ta yadda zai sami yakini kan cewa ya sauke abin da ya rataya a wuyansa.
T527: Mene ne hukuncin ayyukan ibadu misali salla da azumi na mutumin da cikin jahilci ya kasance ba ya kula da jerantawa a cikin wankan janaba?

A: Idan har wannan rashin jerantawa ya kasance ne ta yadda har zai bata wankan, kamar a ce ya gabatar da wanke bangaren dama a kan wanke kai da wuya, ko kuma ya gabatar da wanke bangaren hagu a kan na dama, to dole ne ya rama sallolin da ya sallace su da janaba, to amma azuminsa ya inganta matukar dai a waccan Lokacin yana ganin wankan nasa ingantacciya ce.
T528: Mutum da yake so ya rama salloli na shekara guda, ta yaya ne ya wajaba ya rama su?

A: Zai iya farawa da daya daga cikin sallolin kuma ya yi ta kamar yadda yake yin salloli na farilla guda biyar.
T529: A wani lokaci bayan na yi aure wani ruwa ya kan fitomin wanda a lokacin ina jin cewa najasa ne. Don haka na kan yi wankan janaba sannan kuma in yi salla ta ba tare da alwala ba. To amma a cikin Risalatul amaliyya na ga ana kiran wannan ruwa da sunan mazi. A halin yanzu ban san mene ne hukumcin sallolin da na yi ba tare da alwala ba da jin cewa ina da janaba a jiki na?

A: Wajibi ne ka rama dukkanin sallolin da ka yi ba tare da alwala ba sai dai kawai da wankan da ka yi kana zaton kana da janaba.
T530: Kafirin da daga baya ya musulunta, shin wajibi ne ya rama salloli da azumin da bai yi ba lokacin kafircin nasa?

A: A'a ba wajibi ba ne
T531: Wani mutum ne Allah ya yi masa rasuwa alhali yana da azumin watan Ramalana da kuma sallolin (farilla) a wuyansa sannan kuma ga shi ba shi da namiji. Don haka (kafin rasuwarsa) sai ya ware wasu kudade wadanda za su iya biyan ko dai sallolin da suke kansa ne ko kuma azumin da suke kansa ne kawai (wato ba za su iya biyan dukkanin biyun ba) to a irin wannan yanayi azumi ne za a gabatar ko kuma sallar?

A: Lamarin ba wai fifita salla ko azumi ba ne sannan kuma ba wajibi ba ne a kan magadansa su yi amfani da abin da ya bari wajen biya masa azumi ko sallar da suka kubuce masa ba, sai dai idan ya yi wasiyya ne da hakan wanda a irin wannan yanayi kan wajibi ne a yi aiki da wasiyyar tasa matukar ba ta wuce kashi daya cikin uku na abin da ya bari din ba wajen biya masa abin da ya sawwaka na azumi da sallar.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Ring ring