T542: Wace irin niyya ce limamin da zai jagoranci sallar jam'i zai daura? Shin zai yi niyyar sallar jam'i ne ko kuma zai daura niyyar salla shi kadai ne.
A: Idan har yana son ya samu falalar sallar jam'i, to wajibi ne ya yi niyyar limanci da kuma sallar jam'i. Idan kuwa ya fara sallar ba tare da niyyar limanci ba, sallarsa da ta wadanda suka bi shi babu matsala cikinta.
T543: Shin tsayar da sallar jam'i ta biyu kusa da wani wajen da ake sallar jam'i tare da mutane masu yawa sannan kuma ana ma jin sauti kiran salla da ikamar sallar a wancan wajen tana inganta?
A: Babu matsala cikin tsayar da sallar jam'i ta biyun, to sai dai abin da ya dace shi ne muminai su hadu waje guda su yi sallar jam'i tare don a samu damar kara irin girma da daukakar da sallar jam'i take da ita.
T544: Wasu mutane sukan zo su kabbara sallarsu su kadai a daidai lokacin da ake sallar jam'i a wajen, mene ne hukumcin wannan aikin?
A: Matukar dai wannan aiki zai raunana sallar jam'i da kuma cin mutumcin limamin da jama'a suka amince da adalcinsa ne, to bai halalta ba.
T:545 Akan samu wani waje (unguwa) wanda yake da masallatai sama da guda kuma a kowane guda daga cikin masallatan ana yin sallar jam'i a cikinsa, sannan kuma har ila yau a tsakanin masu masallatai biyu akan samu wasu gidajen da su ma a cikinsu ana yin sallar jam'i, to shin mene ne hukumcin wadannan salloli na jam'i da ake yi?
A: Yana da kyau a dauki sallar jam'i a matsayin wata hanya ta hada kan mutane ba wai hanya ta rarraba kan al'umma ba. Ala kulli hal tsayar da sallar jam'i a cikin gidan da ke makwabtaka da masallaci matukar dai ba za ta haifar da rarrabuwan kai da rikici ba, babu matsala cikin hakan.
T546: Shin ya halalta mutum ya ja sallar jam'i a wani masallaci da aka nada wani limani ratibi ba tare da izinin wannan limami ratibin ba?
A: Tsayar da sallar jam'i ba ta dogara kan izinin limami ratibi ba, to sai dai bai kamata wani ya dami wannan limami ratibi ba a masallacin da aka nada shi limanci a cikinsa matukar dai yana nan. Idan kuwa har hakan zai iya janyo fitina da rikici da makamantan hakan, to haramun ne ma.
T547: Idan a wani lokaci wani limanin jam'i ya fadi wata magana wacce ba ta dace da matsayi irin na malamin addini ba, to shin hakan yana kawar da adalcin da yake da shi?
A: Matukar dai hakan ba ta saba wa shari'a ba, ba ta cutar da adalcinsa ba.
T548: Shin bin limamin da mutum bai san hakikaninsa ba yana halalta?
A: Matukar adalcinsa ya tabbata ga masu binsa salla ta kowace hanya ce kuwa, to binsa yana halalta sannan kuma sallar jam'in da aka yi a bayansa ingantacciya ce.
T549: Shin bin limamin da ba ya umurnin da kyawawan ayyuka da hani da munana alhali kuwa zai iya yin hakan yana halalta?
A: Mujarradin barin umurni da kyawawan halaye da hani da munana ba ya cutar da adalci limami ko kuma rashin ingancin bin bayansa a salla saboda mai yiyu yana da wani uzuri wanda abin karbuwa ne a wajen wannan mukallafin.
T550: A wajenka mece ce ma'anar adalci?
A: Adalci yana nufi wani yanayi na mutum wanda a koda yaushe zai sanya shi kula da tsoron Allah da kuma hana shi barin wajibai ko kuma kutsawa cikin abubuwan da shari'a ta haramta. Kyakkyawan zahiri na mutum kuwa yana tabbatar da hakan.
T551: Shin mutane biyu suna iya tsayar da sallar jam'i?
A: Idan har abin nufi (cikin tambayar) shi ne tsayar da sallar jam'i na limami guda da kuma mamu guda, to babu wata matsala cikin hakan.
T552: Idan a sallar jam'i na azahar da la'asar mamu ya karanta Fatiha da wata sura don daidaitar da hankalinsa waje guda duk kuwa da cewa hakan ba wajibi ba ne a gare shi, to mene ne hukumcin wannan salla tasa?
A: Cikin sallar da wajibi ne a yi karatu a boye kamar sallolin azahar da la'asar, yin karatu a gare shi ba ya halalta ko da kuwa don daidaita hankalinsa waje guda ne.
T553: Yayin sallar jam'i lokacin da liman yake cikin raka'a ta uku ko ta hudu a sallar lisha, shi kuwa mamu yana raka'a ta biyu ce, to shin wajibi ne ya yi karatun (Fatiha da sura) a bayyane?
A: Bisa wannan tambaya wajibi ne ya karanta Fatiha da Sura a boye.
T554: Idan mutum ya iso masallaci alhali ana cikin raka'a ta biyu ne ta sallar jam'i, to sakamakon jahilcin da yake da shi kan hukumcin hakan sai ya yi tashahhud (tahiya) da kunuti wadanda a raka'a ta gaba ce ya wajaba ya yi su, shin sallarsa ta inganta?
A: Na'am sallarsa ta inganta. To sai dai wajibi ne ya rama tahiyar da kuma yin raka'oi biyu na rafkanwa saboda barin tahiyar da ya yi.
T555: Shin neman yarda da amincewar mutumin da za a bi shi salla sharadi ne? Sannan kuma shin bin mamu ya halalta?
A: Neman yardar limamin da za a bi sallar jam'i ba sharadi ne na inganci bin liman ba. Bin mamun da yake bin wani limami ba ya halalta.
T556: Mutane biyu ne suke salla, dayansu liman dayansu kuma mamu, sai wani mutum na uku ya zo zai bi su, to amma sai ya zaci mutum na biyu (wato mamun) shi ne limamin don haka sai ya yi niyyar binsa sallar. Sai bayan an idar da sallar sai ya fahimci cewa ai mamun ya bi ba limamin ba. To mene ne hukumcin sallar mutumi na uku?
A: Bin mamu dai bai inganta ba, to amma a lokacin da ya zamanto mutum bai sani ba sai ya bi shi salla, to matukar dai a lokacin ruku'u da sujada ya yi aiki da abin da ya ke wajibinsa ne wato bai rage ko kara wani rukuni na salla da gangan ko bisa kuskure ba, sallarsa ta inganta.
T557: Mutumin da yake son yin sallar lisha, shin zai iya bin mutumin da yake yin sallar magariba?
A: Babu matsala cikin hakan.
T558: Idan dukkanin mutanen da suke daya daga cikin sahun salla mutane ne da suke kasaru sannan kuma mutanen da suke sahun da ke bayansu dukkansu suna cika salla ne. Idan mutanen da suke sahun dake gaban suka yi sallama bayan raka'oi biyu sai suka mike ba tare da bata lokaci ba don sake yin raka'oi biyun da suka sauran, to shin raka'oi biyu na karshen na mutanen da suke sahun da ke bayansu za su ci gaba da zama cikin sallar jam'i ne ko kuma sallar mutum guda?
A: A irin wannan yanayi na cewa dukkanin mutanen da suke sahun gaba masu kasaru ne, to akwai matsala cikin ingancin sallar jam'in mutanen da suke sahun da ke bayansu. Ihtiyati shi ne cewa mutanen da suke sahun baya, bayan da na gabansu suka yi sallama, su mai da sallarsu zuwa ga matsayi na mutum guda.
T559: Mutumin da ya bi limamin da yake cikin raka'a ta uku alhali shi kuma yana tsammanin raka'ar farko ce, don haka sai bai yi karatu ba, to shin sake sallar ya zama wajibi a gare shi?
A: Idan har ya fahimci hakan kafin ya tafi zuwa ga ruku'u to wajibi ne ya yi wannan karatun, in kuwa bayan ya shiga ruku'u ne ya fahimci hakan, to sallarsa ta inganta kuma babu wani abin da ya hau kansa, ko da yake ihtiyati na mustahabi shi ne ya yi sujadar rabkanuwa saboda barin karatu.
T560: Mutumin da yake takalidi da marigayi Imam Khumaini (r.a) cikin sha'anin sallar matafiyi, shin zai iya bin limamin sallar jam'in da yake takalidi da wani marja'i kan hakan, musamman ma dai a sallar juma'a?
A: Sabanin takalidi ba ya hana ingancin bin wani limami. To amma bin sallar jam'in da marja'in mamun yake ganinta a matsayin kasaru ce sannan kuma bisa fatawar marja'in limamin ana cika ta ne ko kuma akashin haka ba ta inganta ba.
T561: Idan limami bisa mantuwa ya tafi zuwa ruku'u bayan da ya yi kabbarar harama, to a irin wannan yanayi me ya kamata mamu su yi?
A: Idan mamu ya fahimci hakan ne bayan ya fara sallar jam'in kafin ya yi ruku'u to wajibi ne ya sauya niyyarsa zuwa ga sallar mutum guda, sai ya karanta fatiha da sura.
T: 562: Shin taimamar da wani liman zai yi maimakon wanda saboda wani uzuri da yake da shi ta wadatar masa wajen jan salla?
A: Matukar dai wannan uzuri nasa uzuri ne da shari'a ta yarda da shi yana iya limanci da taimamar da ya yi maimakon wanka sannan kuma binsa babu matsala cikinta.