XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Ramakon Salla Ga Mahaifi Da Mahaifiya
Ali Khamenei4

T532: Mahaifina ya fuskanci matsalar tsayawar kwakwalwarsa daga aiki ne na tsawon shekaru biyu ta yadda ba ya iya gane abu mai kyau da mara kyau, wato ba shi da karfin yin tunani. Tsawon wadannan shekaru biyu kuwa bai yi salla da azumi ba. To shin wajibi ne in rama masa wadannan salloli da azumi da bai yi ba a matsayina na babban dansa? Koda ya ke na san cewa idan da ba shi da wannan cutar da wajibi ne in rama masa wadannan salloli da bai yi ba. Ina fatan za ka min karin bayani kana bin da ya kamata in aikata.

A: Matukar wannan rauni na hankali da ya ke da shi bai kai matsayin hauka ba, sannan kuma kawuwar hankalin nasa ba ta kasance na dukkan lokaci ba, to wajibi ne ka rama masa salloli da azumin da suka kubuce masa. Amma idan ba haka ba to babu wani abin da ya hau kanka.
T533: Idan mutum ya rasu rama azumin kaffaran da ya bari yana kan wane ne? Shin wajibi ne a kan ‘ya'yansa maza da mata su yi masa, ko kuwa yana yiwuwa wani mutum na daban ya yi masa?

A: Kaffaran azumi da ke kan mahaifi idan har ‘yar zabi ce wato ko ya yi azumi ko ya ciyar, kuma yana da halin yin biyun duka to idan zai yiwu a cire ta daga cikin abin da ya bari na gadonsa sai a cire, in kuwa ba zai yiwu ba, to a bisa ihtiyati yin azumin yana kan babban da ne.
T534: Wani mutum ne mai shekaru amma saboda wasu dalilai ya rabu da iyalan sannan kuma ba shi da hanyar da zai iya samun labarinsu sannan kuma shi ne babban dan mahaifinsa. To tsawon wadannan shekaru sai mahaifin nasa ya rasu, to amma bai san yawan adadin salloli da sauransu da mahaifin nasa bai yi ba sannan kuma ba shi isassun kudaden da zai bayar wajen a biya wa mahaifin nasa sallolin da suke kansa kamar yadda kuma shi da kansa ba zai iya ramakon ba saboda yawan shekarun da yake da shi. To a nan mene ne ya hau kansa?

A: Ramakon sallar mahaifi ba wajibi ne ba ne face dai kan gwagwardon abin da babban dan nasa yake da yakini kansu. To a nan kan wajibi ne a kansa ya rama masa su ta kowace hanyar da ta sawwaka masa. Idan kuma ba zai iya ramakon ba hatta ta hanyar daukan hayar wani mutum ya yi, to yana da uzuri.
T535: Idan babban dan mutum mace ce, na biyun ne namiji, to shin ramakon salla da azumin mahaifiya da mahaifinsa suna kansa (yaron) ne a wannan halin ma?

A: Abin lura a cikin wannan al'amari shi ne babban da namiji daga cikin ‘ya'yaye mazaje idan har mahaifinsa yana da 'ya'ya maza. To dangane da wannan tambaya, ramakon salla da azumin mahaifi haka ma mahaifiya yana kan wannan da na biyun ne.
T536: Idan babban da, bakagagge ne shi ko kuma ba balagagge ba, ya rasu kafin rasuwar mahaifinsa, to shin ramakon sallar mahaifi ya fadi daga kan sauran ‘ya'yan kenan?

A: Wajibcin ramakon salla da azumin mahaifa yana wajaba ne kan babban dan da ya kasance a raye yayin rasuwar mahaifan ko da kuwa ba shi ne dan farko ga mamacin ba.
T537: Ni ne ban da a gidanmu. To shin wajibi in tambayi mahaifina adadin abubuwan da suke kansa (na salla da azumi) saboda in san abin da zan rama masa na salloli da azumi? Idan kuma bai sanar da mu ba, wani nauyi ne ya ke kaina?

A: Bincike da tambaya ba wajibi ba ne a kanka, to amma wajibi ne shi kansa mahaifin matukar yana da daman yin haka ya yi salloli da azumin da ke kansa, idan kuwa ba zai iya ba to ya yi wasicci da hakan. Ala kulli hal, wajibi ne babban da ya rama wa mahaifansa abin da yake da yakinin cewa ba su yi ba.
T538: Idan babban dan da nauyin rama salloli da azumin da mahaifansa suka bari yake wuyansa ya rasu, to shin wajibcin rama wadannan salloli yana komawa ne da ‘ya'yansa ko kuma yana komawa ne ga wanda yake biye masa?

A: Ramakon salloli da azumin da suke wuyan babban dan mamaci ba sa komawa wuyan dan babban dan ko kuma wani mutum na daban idan har ya rasu ne bayan rasuwar mahaifin nasu.
T539: Mahaifin da bai taba yin salla ba, to shin ramakon dukkanin wadannan salloli suna wuyan babban dansa ne?

A: Bisa ihtiyati a irin wannan yanayi ma ramakonsu wajibi ne.
T540: Mahaifin da ya bar dukkan ayyukansa na ibada da gangan, to shin wajibi ne ga babban dansa ya rama masa dukkan wadannan ayyukan wadanda sun kai ayyukan shekaru hamsin?

A: Matukar ya bar sallolin ne saboda dagawa, to ramakonsu ba wajibi ba ne a kan babban dan. Ko da yake yana da kyau dai ya rama masa bisa ihtiyat.
T: 541: Mahaifi na yana da ramakon salla a kansa, sannan kuma ba shi da karfin da zai rama din. To shin ya halalta a matsayina na babban dansa in rama masa wadannan salloli da bai yi alhali yana raye ko kuma in dau hayar wani mutum ya yi masa?

A: Bai inganta a rama wa wani mutum da yake raye salla da azumin da ke kansa ba.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din