XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Bin Ahlussunna Sallah
Ali Khamenei4

T599: Shin bin Ahlus sunna salla ya halatta?

A: Na'am, salla a bayansu ta halatta.
T600: A wasu wajaje da muke muna rayuwa da aiki ne tare da ‘yan Ahlussunna, to a lokacin salla mu kan yi salla tare da su sannan kuma mu kan yi yadda suke yin salla ne, a matsayin misali mu kan yi kama kirji (kabalu) da kuma yin salla a lokacinsu da kuma sujada a kan darduma. To shin (wannan sallar ta inganta) ko kuma sai mun sake wannan salla.

A: Idan har hakan yana iya tabbatar da kare hadin kan musulmai to salla tare da su ta inganta kana ta wadatar ko da kuwa da yin sujada akan darduma da makamantan hakan ne. To amma yin kabalu a salla tare da su bai halatta ba sai dai idan a bisa lalura ne.
T601: Yayin da muke salla da Ahlussunna a masallatansu to shin mene ne hukuncin harhada kananan yatsun kafafu da gefen kafafu da suke yi yayin da suke tsaye?

A: Wannan aiki dai ba wajibi ba ne, to amma yin hakan ba ya bata bata salla.
T602: ‘Yan'uwa ‘yan Ahlussunna a lokacin aikin hajji da ma sauran lokuta su kan yi sallar magariba ne kafin shigan lokaci (wato lokacin sallar magariba kamar yadda fikihun Shi'a ya yi bayani), to shin muna iya binsu salla sannan kuma hakan ya wadatar?

A: Bai dai tabbata ba cewa suna yin sallar kafin lokaci, to amma matukar dai mutum ya tabbatar da cewa lokaci bai shiga ba, to ba zai iya yin salla ba, sai dai idan saboda kiyaye hadin kan musulmi ne. A irin wannan yanayi kan ana iya yin salla tare da su sannan kuma ta wadatar babu wata matsala cikin hakan.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din