BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Fushi Da Zafin Rai
Daga cikin wa'azozin
Manzon Allah (s.a.w.a)
akwai cewa:
ﻭﻗﺎﻝ ﺭﺟﻞٌ ﺍَﻭْﺻِﻨﻰ، ﻓﻘﺎﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠّﻢ: ﻻﺗَﻐﻀَﺐ،
ﺛﻢ ﺃﻋﺎﺩَ ﻋﻠﻴﻪ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻻﺗَﻐﻀَﺐ، ﺛﻢّ
ﻗﺎﻝ: ﻟﻴﺲ ﺍﻟﺸّﺪﻳﺪ ﺑِﺎﻟﺼّﺮَﻋَﺔِ، ﺍﻧّﻤﺎ
ﺍﻟﺸﺪﻳﺪُ ﺍﻟﺬﻱ ﻳَﻤﻠﻚُ ﻧﻔﺴﻪ ﻋﻨﺪ
ﺍﻟﻐﻀﺐِ
"Wani mutum ya zo wajen
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce
ka yi mini wasiya, sai
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce
masa: kada ka yi fushi, sai
mutumin ya sake dawowa
yace ka yi mini wasiya,
Manzon Allah ya ce kada ka
yi fushi. Sannan Manzon
Allah ya kara da cewa karfi
ba shi ne mutum ya yayi
galaba a kokuwa ba, karfi
shi ne mutum ya mallaki
zuciyarsa yayin fushi".
(Tuhaful-Ukul shafi na 47)
Abin da ake nufi da kalmar
"kada ka yi fushi" ba wai shi
ne fushin da yafi karfin
iradar mutum ba (wanda ya
fita daga zabinsa). Abin nufi
shi ne fushin dake
karkashin zabin mutum,
wato kada mutum ya rufe
idonsa yayi amfani da fushi
wajen fuskantar al'amurra.
Mutum mai karfi ba shi ne
wanda ya samu nasarar
kayar da abokin kokawarsa
ba, amma mai karfi shi ne
wanda lokacin da yayi fushi
yake amfani da basira da
hankali wajen mallakan
kansa da kwantar da
fushinsa.
Har ila yau abin nufi da
fushi ba shi ne fushi mai
saurin gushewa ba kawai,
har ma da fushin da mutum
ke hadiye shi yana neman
damar da ta dace domin ya
dau fansa kan wanda ya
bata masa rai.
Hakika hadiye fushi fushi da
kawar da sha'awar da
mutum ke yi yana da tasirin
gaske a dukkanin
rayuwarsa.