Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumcin Limamin Da Bai Iya Karatu Ba
Ali Khamenei4

T563: Shin akwai wani bambanci ne cikin ingancin karatu tsakanin sallar mutum guda da sallar mamu ko kuma na limami? ko kuma ingancin karatu a kowane yanayi lamari ne guda?

A: Idan har karatun mukallafi ba daidai ba ne sannan kuma ba zai iya koyon karatun ba, to sallarsa ta inganta, sai dai sauran mutane ba za su bi shi salla ba.
T564: Karatun wasu daga cikin limaman sallar jam'i ta bangaren fitar da haruffa ba daidai ba ne. To shin mutumin da ya ke iya fitar da haruffa da kyau zai iya bin irin wadannan limamai salla? Wasu suna cewa zai iya binsu salla to amma daga baya wajibi ne ya sake sallar tasa, to sai dai ni da ba na da lokacin yin hakan, wane nauyi ne ya hau kaina? Shin zan iya halartar sallar jam'in amma in karanta Fatiha da Sura a boye?

A: Idan karatun liman a wajen mamu ba daidai ba ne, to sallar jam'insa batacciya ce, idan kuwa har ba zai iya sake sallar ba, to babu matsala cikin rashin bin sallar jam'in. Amma boye karatun sallar da wajibi ne a bayyanar da shi don saboda bayyanar da bin sallar jam'i bai halalta ba.
T565: Yayin da liman yake ba da sallar jam'i sai ya yi shakka cikin fadin wata kalma (wato shin ya fade ta daidai kuwa ko a'a), amma bayan idar da sallar sai ya tabbatar da cewa lalle ya yi kuskure wajen fadin kalmar. Mene ne hukumcin sallarsa da kuma sallar mamun da suka bi shi?

A: Sallarsa ta inganta.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Polly po-cket