BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
Hukumce-Hukumcen Limancin Nakasasshen Mutum
T566: Mene ne hukumcin bin limancin nakasassun mutane masu nakasa kamar haka:
-1 Nakasasshen da ba wai ya rasa wata gaba ta jikinsa ba ne to amma saboda matsalar da yake da ita a kafafunsa sai ya yi amfani da sanda ko dogaro da katanga kafin ya iya tsayawa.
-2 Nakasasshen da ya rasa wasu yatsun hannuwansa ko kafafunsa.
-3 Nakasasshen da ya rasa wani bangare na hannunsa ko kafarsa ko kuma dukkan biyu.
-4 Nakasasshen da ya rasa wani bangare na jikinsa, sannan kuma saboda dalilin matsalar da yake da ita a hannunsa, sai ya nemi taimakon wani kafin ya iya yin alwala.
A: A yanayi na gaba daya matukar dai akwai kwanciyar hankali da tabbatuwa ta dabi'a tattare da mutum yayin tsayawa sannan kuma zai iya kiyaye hakan yayin karatun fatiha da sura da zikirorin salla da sauran ayyukan sallar, sannan kuma yana da karfin yin ruku'u da cikakkiyar sujada ta hanyar sanya dukkanin gabobin nan bakwai a kan kasa kuma zai iya yin sahihiyar alwala, sannan kuma ya cika sauran sharuddan limanci, to babu matsala wajen binsa salla, sallar jam'in ta inganta, amma idan ba haka ba sallar jam'in ba ta inganta ba kuma bai halalta a bi shi salla ba.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved