Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Halartar Mata Sallar Jam'i
Ali Khamenei4

T567: Shin shari'ar Musulunci mai tsarki tana kwadaitar da mata tamkar maza wajen halartar sallar jam'i a masallatai ko sallar juma'a ko kuma tana ganin su yi salla a gidajensu shi ne ya fi?

A: Babu wata matsala cikin halartar mata sallar jam'i da ta juma'a, kuma za su sami ladar sallar jam'i.
T568: A wani yanayi ne mace za ta iya jan sallar jam'i?

A: Mace 'yan'uwanta mata ne kawai za ta iya ja sallar jam'i.
T569: Mene ne hukumcin halartar sallar jam'in mata ta bangaren mustahabbanci da karhanci? Sannan idan suka halarci (sallar jam'in) suka tsaya a bayan maza, mene ne hukumcin hakan? Sannan kuma shin akwai bukatar a sanya wani labule a tsakaninsu da mazan idan har sun tsaya ne a bayansu? Idan kuma sun tsaya ne a gefen maza, mene ne hukumcin hakan? Sannan shin sanya su cikin labule yayin salla ko kuma yin wa'azi da sauran bukukuwa ba zai zamanto kaskanta su da cin mutumcinsu ba?

A: Babu wata matsala cikin halartar sallar jam'in mata, idan kuwa sun tsaya ne a bayan maza to babu bukatar sanya labule. Amma idan har sun tsaya ne a gefen mazan ne to yana da kyau a sanya labule a tsakaninsu don kawar da karhancin dake cikin haduwa waje guda tsakanin maza da mata cikin salla. Dangane da batun cewa zaman mata cikin labule cin mutumci ne da kaskantar da mata ba shi da wani tushe ballantana asasi. Tsoma bakin da sanya mahanga ta mutum cikin fikihu bai inganta ba.
T570: Ya ya yanayin haduwar sahun mata da maza ko rashin haduwarsa cikin salla a lokacin da babu wani labule a tsakaninsu yake?

A: Mata suna iya tsayuwa a bayan maza ba tare da wata tazara ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din