XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hukumce-Hukumcen Sallar Juma'a
Ali Khamenei4

T603: Mene ne fatawarka dangane da yin sallar juma'a ga shi kuma muna zamanin "gaibar" mai girma Al-Hujja (lmam Mahdi), Allah Madaukakin Sarki Ya gaggauta bayyanarsa, ne? Sannan kuma idan mutum bai yarda da adalcin limamin juma'a ba, to shin wajibcin halartan sallar tana faduwa a kansa ne ko kuma a'a?

A: Ko da yake sallar juma'a a wannan lokaci namu wajiba ce 'yar zabi, (wato tsakaninta da sallar azahar) halartarta ba wajibi ba ne, to amma saboda la'akari da falalolin da ke cikinta, bai kamata muminai su haramta wa kansu albarkar da ke cikinta ba don kawai saboda shakkar adalcin liman ko kuma saboda wasu dalilai marasa tushe.
T604: Mene ne ma'anar wajibi dan zabi a mas'alar sallar juma'a?

A: Ma'anarsa shi ne mutum yana da zabi wajen sauke nauyin sallar azahar ta ranar juma'a ko dai ya yi sallar juma'ar ko kuma ya yi sallar azahar.
T605: Mene ne fatawarka kan mutumin da ke barin sallar juma'a saboda rashin daukanta da muhimmanci?

A: Barin halartar sallar ibada da siyasa ta juma'a saboda rashin daukanta da muhimmanci abin zargi ne a shari'a.
T606: Shin tsayar da sallar jam'in azahar a daidai lokacin da ake yin sallar juma'a a wani waje da ke kusa da wajen yana halalta?

A: Shi wannan aiki a kan kansa ba shi da matsala kuma yana wadatar wa mukallafi daga sallar azahar na ranar juma'a saboda a wannan zamani da muke ciki sallar juma'a wajiba ce ‘yar zabi. To amma bisa la'akari da cewa tsayar da jam'in sallar azahar a ranar juma'a a wani waje da ke kusa da inda ake tsayar da sallar juma'a lamari ne da zai haifar da rarrabuwa tsakanin muminai baya ga cewa wasu za su iya fassara hakan a matsayin cin mutumci da rashin girmama limamin juma'ar da kuma rashin kula da sallar juma'a. A saboda haka bai kamata muminai su aikata hakan ba. Kai idan ma har hakan zai iya haifar da fasadi da abin da yake haram to wajibi ne ma a nesanci tsayar da irin wannan salla.
T607: Idan mutum yana ganin limamin juma'a ba adali ba ne, ko kuma yana shakkan adalcinsa, to shin ya halatta ya bi shi salla saboda kiyaye haÉ—in kan musulmi? Kana shin yana halatta ga mutum da ba ya halartar sallar juma'a ya yi kokarin hana sauran mutane halarta?

A: Bin limamin da mutum ba ya ganinsa a matsayin adali ko kuma yake shakkar adalcinsa ba ya inganta haka nan kuma sallar da ya yi a bayansa ba ta inganta ba. To amma halartar sallar jam'i saboda kiyaye hadin kan musulmai babu matsala cikin hakan. To amma ta kowane yanayi bai da damar da zai kwadaitar da wasu a kan barin halartan sallar juma'a. Haka nan kuma bai kamata mutum ya haramta wa kansa albarkokin da ke cikin sallar juma'a saboda kawai tunanin cewa limamin juma'ar ba adali ba ne.
T608: Mene ne hukumcin rashin halartar sallar juma'a da bin limamin juma'ar da mutum ya san cewa shi makaryaci ne?

A: Mujarradin fahimtar cewa abin da limamin juma'a ya fadi ya saba wa hakika ba dalili ba ne na cewa shi makaryaci ne, saboda me yiyuwa ne kuskure ya yi cikin abin da ya fadin ko kuma tauriya ce. Bai kamata don kawai mutum yana zaton adalcin limami ya fadi ya haramta wa kansa samun albarkar da ke cikin sallar juma'a ba.
T609: Yayin da mutum yake shakkar adalcin limamin juma'a ko kuma abin Allah Ya kiyaye ya samu yakinin rashin adalcinsa, to shin wajibi ne ya sake sallolin da ya yi a bayansa?

A: Idan har shakka kan adalcinsa ko kuma yakinin rashin adalcin ya faru ne bayan idar da sallar, to sallolin da ya yi din sun inganta, kuma ba wajibi ba ne ya sake su.
T610: Mutumin da yake sallar kasaru shin zai iya yinta a bayan limamin da yake jan sallar juma'a?

A: Sallar juma'ar mamun da ke halin tafiya ta inganta kuma ta dauke masa sallar azahar.
T611: Shin mutum zai iya yin wata salla ta farilla ta daban a bayan limamin juma'a da yake sallar juma'a?

A: Akwai matsala cikin ingancin wannan salla.
T212: Mutumin da ba shi da damar tafiya sallar juma'a ba, shin zai iya yin sallar azahar da la'asar dinsa tun farkon shigan lokaci ko kuma wajibi ne ya jira sai an idar da sallar juma'a kafin ya yi sallar azahar da la'asar din?

A: Ba wajibi ne ya jira sai an idar da sallar juma'a ba, zai iya yin sallolinsa na azahar da la'asar tun farkon lokaci.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din