T613: A fatawarka sallar idin karamar salla da babbar salla da kuma sallar juma'a daga cikin wani nau'i na wajibi suke?
A: A wannan zamani da muke ciki sallar karamar salla da babbar salla ba wajibi ba ce, mustahabi ce, to amma sallar juma'a wajiba ce ‘yar zabi (ko dai mutum ya yi sallar juma'ar ko kuma ya yi sallar azahar).
T614: Shin kari ko kuma ragi cikin kunutin sallar idi suna bata sallar?
A: Idan har abin nufi da ragi da karin shi ne takaitawa ko tsawaitawa cikin karatun kunutocin da ake yi to hakan ba ya bata su. To amma idan abin nufi da ragi ko karin shi ne ragi ko kari cikin adadin kunutin da ake yi, to a nan dai wajibi ne a yi sallar yadda aka yi bayaninta cikin littafan fikihu.
T615: Shin sallar idin karamar salla tana da ramuko?
A: Ba ta da ramuko.
T616: Shin ana yi wa sallar idi ikama?
A: A'a ba ta da ikama.
T617: Idan limamin da zai ja sallar idin karamar salla ya yi ikama, to mene ne hukumcin sallarsa da ta sauran masallata?
A: Babu abin da zai sami sallar limamin da wadanda suka bi shi.