Snack's 1967
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Wanda Tafiya Ta Kasance Aikinsa Ko Kuma Ta Kasance Matakin Farko Na Aikinsa
Ali Khamenei4

Hukumce-Hukumcen Salla - Wanda Tafiya Ta Kasance Aikinsa Ko Kuma Ta Kasance Matakin Farko Na Aikinsa

T620: Mutumin da tafiya ta kasance matakin farko na aikinsa, shin shi ma zai cika sallarsa ne kuma zai yi azumi ko kuma hakan ya kebanta ne kawai ga mutumin da tafiya ta zama aikinsa ne kawai? Kana mene ne maraja'ai kamar lmam Khumaini (r.a) suke nufi yayin da suke cewa! "Mutumin da tafiya ta kasance aikinsa"? Shin akwai mutumin da tafiya take zama aikinsa? Domin kuwa hatta makiyayi, ko kuma direbobi da dai sauransu aikinsu shi ne kiwo, ko kuma tuki, ba wai tafiya ba, don haka babu wani mutumin da tafiya ita ce aikinsa?

A: Duk mutumin da tafiya ta kasance matakin farko na aikinsa idan har a duk kwana goma zai yi tafiya sau guda zuwa wajen aikin nasa don yin aikin to zai cika salla kuma azuminsa ya inganta. Kana kuma ma'anar mutumin da tafiya ta kasance aikinsa - cikin maganganun malaman fikhu, Allah Ya yarda da su - shi ne duk mutumin da aikinsa bai yiwuwa sai da tafiya-tafiye kamar irin ayyukan da aka ambata a cikin wannan tambaya.
T621: Mece ce fatawarka dangane da salla da azumin mutumin da yake zaune a wani gari na kimanin shekara guda saboda wani aiki ko kuma irin aikin nan na bautan kasa da mutum yake yin shekara guda zuwa shekaru biyu don bautan kasa a wani gari? Shin wajibi ne ya yi niyyar zama na kwanaki goma (zuwa sama) bayan duk wata tafiya da ya yi don ya sami damar cika sallarsa da kuma yin azumi? Sannan kuma idan ba shi da niyyar zama na kwanaki goma fa (wato zai zauna ne na kasa da kwanaki goman), mene ne hukumcin salla da azuminsa?

A: Idan alal akalla zai dinga yin tafiya sau guda cikin kwanaki goma saboda yanayin aikin nasa zuwa wajen aikinsa, to baya ga tafiyar farko sauran tafiyan kan zai cika sallar ne haka nan kuma zai yi azumi. Amma a tafiyar farko hukumcinsa hukumcin sauran matafiya ne, wato matukar dai ba su yi niyyar zama na kwanaki goma ba, to sallarsu kasaru za su yi ta sannan kuma bai inganta su yi azumi ba.
T622: Ni na kasance ma'aikaci ne a wani gari kana kuma daga gidan da nake zaune zuwa wajen aikina ya kai kimanin kilomita 35 ne, haka kullum na ke wannan tafiya kafin in isa ga wajen aikin nawa, to ya ya sallata za ta kasance lokacin da nake da wani abu na musamman (wanda ba ya daga cikin aikin nawa) a wannan gari kana kuma zan zauna a wajen na wasu ranaku. To shin zan cika salla ne ko kuma kasaru zan yi?

A: Idan har tafiyar ba saboda wannan aikin naka wanda kullum kake tafiya saboda shi ba ne, to wannan tafiya ba ta da hukumcin matafiyin da tafiya ita ce aikinsa. To amma idan har tafiyar saboda wannan aiki naka ne, kuma ko da yayin da kake wannan gari za ka yi wani abu na daban kamar ziyarar dangi, ta yadda har ma wani lokaci za ka kwana ko ma kwanaki a wajen, to wannan hukunci dai na matafiyin da tafiya ita ce aikinsa yana nan a kanka, wato za ka cika salla kana za ka yi azumi.
T623: Bayan an tashi aiki da kuma gama ayyukan da saboda su ne nake yin tafiya wajen aiki na a wani gari na kan yi wasu ayyuka kuma na daban na kashin kaina. A matsayin misali ina yin ayyukana ne na ofis tun daga karfe bakwai na safiya zuwa karfe biyu na rana sannan daga nan kuma sai in shiga sauran ayyukan na kashin kaina. To a nan mene ne hukumcin salla da azumi na?

A: Yin ayyuka na kashin kai yayin tafiya ta aikin ofis bayan gama aikin (ofis din) ba ya sauya hukumcin tafiya ta aiki.
T624: Cikin Risalatul Amaliyya ta marigayi Imam Khumaini a bangaren sallar matafiyi, sharadi na bakwai ya zo cewa: "Wajibi ne direba a sauran tafiyarsa ban da ta farko ya cika sallarsa amma a tafiyar farko zai yi kasaru ne komai nisanta kuwa. To shin tafiyar farko tana nufin tashi daga garin mutum har zuwa lokacin da zai dawo ne ko kuma daga lokacin da ya isa inda zai je shi kenan hukumci tafiyar farko ya kare?

A: Idan har tafiya da dawowa a mahangar mutane ana kirgata a matsayin tafiya guda ce, wato misali malamin da ya ke tafiya wani gari don karantarwa sannan kuma da yamma ko kuma washegari ya dawo, to a irin wannan yanayi ana kirga tafiya da dawowar a matsayin tafiyar farko. Amma idan har a mahangar jama'a ba a ganin hakan a matsayin tafiyar farko, misali direban da ya dau kaya daga garinsu zuwa wani waje kana daga can kuma ya dauki fasinja ko wani kayan na daban kuma zuwa wani waje na daban sannan daga karshe kuma ya dawo gida. To a irin wannan yanayi kan tafiyarsa ta farko ta kan kare ne a lokacin da ya isa wajen da ya yi niyyar tafiya (na farko).
T625: Mutumin da tuki ba shi ne asalin aikinsa ba, to amma sai aka ba shi aikin tuki na wani lokaci, a matsayin misali irin masu bautan kasa din nan da a sansaninsu a ke ba su aikin tuki. To shin irin wadannan mutane hukumcin matafiyi ko kuma wajibi ne su cika sallarsu sannan kuma su yi azumi?

A: Idan har a mahangar jama'a tukin mota na dan wannan lokaci ana iya kirga shi a matsayin aikinsu, to hukumcinsu daidai ya ke da hukumcin sauran direbobi.
T626: Idan motar wani direba ta samu wata matsala da ta sanya ta tsayawa na wani dan lokaci, to don gyaranta ya zama wajibi direbanta ya tafi wani gari na daban don sayo wasu kayayyakin da ake bukata. To bisa la'akari da cewa ba da wannan motar tasa ya tafi ba, to a irin wannan tafiya ya ya zai yi sallarsa, shin zai cika ne ko kuma zai yi kasaru?

A: Matukar aikinsa a yayin wannan tafiya ba shi ne tuki ba sannan kuma mutane ba sa ganin wannan tafiyar tasa a matsayin tafiya ta aiki, to hukumcinsa daidai ya ke da hukumcin sauran matafiya.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din