T34: Wani mutum bayan rasuwar Imam al-Rahil (r.a) ya yi takalidi wa wani marja'i, to amma a yanzu yana so ya sake komawa ga taklidin Imam (r.a) a karo na biyu, shin hakan ya halatta a gare shi?
A: A bisa ihtiyat canza takalidi daga rayayyen mujtahidi wanda ya cika sharudda zuwa ga mamaci ba ya halatta, na'am idan har shi rayayye bai mallaki sharuddan takalidi ba to komawa gare shi tun farko bai inganta ba, dan haka kenan har yanzu yana nan a kan taklidin waccan mamacin kuma yana da zabi imma dai ya ci gaba da taklidin mamacin ko kuma ya koma ga rayayyen mujtahidi wanda ya halatta a yi masa takalidi.
T35: Mene ne hukuncin ci gaba da takalidin mamaci idan har mamacin shi ne A'alam?
A: Bisa dukan hali ci gaba da takalidin mamaci ya halatta ko da yake ba wajibi ba ne, to amma ya kamata kada abar lhtiyat wajen ci gaba da takalidin mamacin da yake shi ne A'alam.
T36: Shin neman izinin A'alam wajen ci gaba da takalidin mamaci sharadi ne ko kuma za'a iya neman izinin kowane mujtahidi?
A: Ba wajibi ba ne takalidin A'alam cikin mas'alar ci gaba da takalidin mamaci, idan dukkan fukaha'u sun yarda da hakan.
T37: Bayan rasuwar lmam (r.a) na zaci cewa ba ya halatta a ci gaba da taklidin mamaci kamar yadda fatawarsa ta nuna, don haka sai na zabi wani mujtahidi rayayye don in masa taklid to shin ya halatta in sake komawa ga lmam (r.a) a karo na biyu?
A: Ba ya halatta gare ka ka koma gare shi (Allah ya rahamshe shi) bayan ka canza takalidinka cikin dukkan mas'alolin fikihu daga gare shi zuwa ga wani rayayyen mujtahidi, sai dai idan fatawar shi wannan rayayyen mujtahidi ita ce wajibcin ci gaba da takalidin mamacin da yake A'alam kana kuma kai ka yarda da cewa Imam (r.a) shi ne A'alam kan wannan rayayyen mujtahidi, to a wannan hali wajibi ne gare ka ka ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a).
T38: Shin wajibi ne ga masu takalidin Imam (r.a) kana kuma suke son ci gaba da yi masa takalidi su nemi izinin daya daga cikin rayayyun maraji'ai ko kuwa ittifakin da yawa daga cikin maraji'ai da manyan malamai kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar?
A: Ittifakin manyan malaman wannan zamani kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar wajen ci gaba da takalidin marigayi lmam (r.a) dan haka babu bukatan sai an koma ga wani takamammen mujtahidi.
T39: Mene ne fatawarka kan ci gaba da takalidin mamaci cikin mas'alolin da mukallafi ya yi aiki da su yayin rayuwarsa da kuma wanda bai yi aiki da su ba?
A: Ci gaba da takalidin mamaci cikin dukkan mas'aloli har ma wanda shi mukallafi bai yi aiki da su ba ya halatta kuma yana isarwa.
T40: Mun kasance masu takalidin lmam Khumaini (r.a) kana kuma muka ci gaba da yi masa takalidi bayan rasuwarsa, to yana iya yiyuwa wata mas'ala ta sharia ta bijiro mana musammam ma ga shi muna raye ne a zamanin manyan azzalumam duniya, dan haka sai muka ga yana da muhimmanci mu koma gare ka cikin dukkan masalolin sharia, a dalilin haka muke so mu komo gare ka mu yi maka Takalidi, shin za mu iya hakan?
A: Ya halatta muku ku ci gaba da takalidin marigayi lmam (r.a), babu wata bukatan ku canza takalidinku daga gare shi (r.a), to idan har wata bukatan neman hukuncin shari'a kan wasu sababbin mas'aloli ta taso, to kuna iya tuntubar ofishinmu, Allah ya shiryar da ku zuwa ga yardarsa.
T41: Mene ne abin da ya wajaba kan mai yin takalidi ga wani marja'i yayin da A'alamiyyar wani marja'i ta bayyana masa?
A: Wajibi ne bisa ihtiyat ya koma zuwa ga marja'in da ya gano A'alamiyyarsa -cikin mas'alolin da fatawar wannar marja'i nasa suka saba da na shi wannan marja'i Aalam.
T42: A wani hali ne ya halatta ga mukallafi ya canza marja'in da yake masa takalid?
A: Canza takalid yana wajaba ne bisa ihtiyat idan shi marja'i na biyun ya fi na farkon sani, kana fatawarsa cikin mas'ala ta saba wa ta farko, to amma idan dai-dai suke to a bisa lhtiyat ba ya halatta.
T43: Shin ya halatta komawa zuwa ga wanda ba A'alam ba idan fatawoyin shi marja'i A'alam ba su dace da zamaninsu ba ko kuma aiki da su yana da wahalar gaske?
A: Bai halatta ba Canza takalid daga A'alam zuwa ga wani mujtahidi saboda kawai zaton rashin dacewar fatawoyinsa da irin yanayin da ke kewaye da su, ko kuma dan kawai kasantuwar akwai wahala cikin aiki da wadannan fatawoyi.