MAS'ALOLI DABAN- DABAN KAN TAKALIDI T44: Mene ne ma'anar jahilul mukassir?
A: Jahilul mukassir: Shi ne jahilin da ya san shi jahili ne, kuma ya san hanyoyin da zai iya bi wajen kawar da jahilcin amma ya ki ya bi su.
T45: Wane ne kuma Jahilul Kaasir?
A: Al-Jahilul Kaasir: Shi ne wanda bai fadaka da jahilcinsa ba, ko kuma bai san hanyar da zai bi wajen kawar da jahilcin nasa ba?
T46: Mene ne ma'anar ihtiyati na wajibi?
A: Ma'anarsa shi ne wajibi ne ayi aiki ko abar aikata wani aiki saboda ihtiyati (ko kuma a koma ga wani marja'i).
T47: Shin wannan lafazi ta "fihi ishkal" (akwai matsala a cikinsa) wanda ake kawo shi a cikin fatawoyi yana nufin haramci ne?
A: Ma'anarta tana banbanta gwargwadon yadda ta zo, idan har matsalar a wajen halacci ne to tana nuna haramci ne a fagen aiki.
T48: Shin wadannan ibarori: "Fihi lshkal", "mushkil" "la yakhlu min lshkal" (wato bai fita daga cikin matsala ba) "la ishkal fihi" (wato babu matsala a cikinsa) fatawoyi ne ko kuma ihtiyat ne?
A: Dukkansu ihtiyati ne in banda ibarar "la ishkal fihi" ita fatawa ce.
T49: Mene ne banbanci tsakanin rashin halacci da haramun?