BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Kaddara
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
ﻋﺠﺒﺎً ﻟﻠﻤﺆﻣﻦ ﻻﻳﻘﻀﻲ ﺍﻟﻠّﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻗﻀﺎﺀً ﺇﻻ ﻛﺎﻥ ﺧﻴﺮﺍً ﻟﻪ، ﺳﺮّﻩ ﺍﻭ
ﺳﺎﺀﻩ. ﺇﻥ ﺍﺑﺘﻼﻩ ﻛﺎﻥ ﻛﻔّﺎﺭﺓً ﻟﺬﻧﺒﻪ،
ﻭﺇﻥ ﺍﻋﻄﺎﻩ ﻭﺃﻛﺮﻣﻪ ﻛﺎﻥ ﻗﺪ ﺣﺒﺎﻩ
"Abin mamaki ga mumini,
Allah ba Ya biya masa wata
bukata har sai ta zame
alheri gare shi, ta faranta
masa rai ne ko ta bakanta
masa. Idan ya jarabce shi ya
kasance kaffara ce ga
zunubansa, idan kuma ya
biya masa (bukatar) ya
kuma karrama shi, to hakan
kyauta ce gare shi".
(Tuhaful-Ukul shafi na 48).
Duk abin da Allah
Madaukakin Sarki Ya
kaddara wa mumini alheri
ne gare shi. A wasu lokuta
wani lamari ya kan taso
wanda zai bakanta masa
rai, misalin rashin lafiya, a
wasu lokutan kuma wani
lamari ya kan faru ya
faranta masa rai. To lamarin
da ya zame abin bakin ciki,
kaffara ce ga zunubansa.
Lamarin da ya zama abin
farin ciki kuwa gare shi
kyauta ce ta Ubangiji.
Ma'anar wannan hadisi ya
zo cikin wakar Hafiz
(Shirazi) da ke cewa duk
abin da ya zo a hanyar Sufi
alheri ne gare shi. Sai dai
Hafiz ya takaita ma'anar ce
ga Sufi, amma a wannan
hadisi ana magana ce kan
duk wani mumini.