Duck hunt
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali


MARJA'ANCI DA WILAYA

Ali Khamenei4

T50: A shar'ance mene ne ya wajaba kan musulmai kana kuma mene ne ya wajaba su aikata lokacin da aka sami sabani tsakanin fatawar shugaban musulmai (waliyu amril muslimin) da fatawar wani marja'i cikin mas'alolin zamantakewa, siyasa da al'adu? Shin akwai haddi da ke banbance hukunci da ya fito daga wani marja'i da kuma wanda ya fito daga "waliyul Fakih"? misali idan ra'ayin wani marja'i kan sauraren kida ya saba da ra'ayin "waliyil fakih", shin a cikinsu wanne ne ya zama wajibi a bi shi kana wanne ne bin sa ke wadatarwa?

Abin nufi a nan dai shin wadansu hukunce-hukunce ne ake kira "Ahkamul Hukumatiyya" (wadanda) hukuncin "waliyul fakih" a cikinsu yana da fifiko kan fatawar marja'i?

A: Fatawar waliyu amril muslimin ita ce za a bi (kuma ita ce abin bi) a lamurran da suka shafi hukuma da hukuncin kasa ta Musulunci haka nan fatawarsa ita ce abin bi cikin ababen da suka game musulmai duka amma lamurran da suka shafi daidaikun mutane, to kowane baligi zai iya tuntubar marja'insa a kansu.
T51: Misali idan na kasance ina takalidi wa wani marja'i, sai "waliyu amril muslimin" ya ba da umurnin fita yaki dan fuskantar kafirai azzalumai ko kuma ya wajabta jihadi, to amma marja'in da nake masa takalidi bai ba ni izinin shiga yakin ba, to shin zan bi ra'ayinsa ne ko kuma a'a?

A: Wajibi ne yin biyayya ga umarnin wali amril muslimin cikin al'amurran da suka game musulmai wanda kare addinin Musulunci da musulmai yana daga cikin wadannan lamurra, domin kare su daga kafirai da azzalumai da suka kawo hari ma musulmai.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din