BABIN WILAYATUL FAKIH DA KUMA HUKUNCIN SHUGABA (JAGORA)
T52: Shin za'a iya daukar mutumin da bai yarda da 'wilayatul fakih na mutlaki ba da cewa shi musulmi ne hakika?
A: Rashin yarda da wilayatul fakih na mutlaki a zamanin gaibar Imam Mahdi (A.F), bai sa mutum ya yi ridda kuma bai fitar da mutum daga Musulunci sawa'un ijtihadinsa ne ya kai shi ga haka, ko kuma taklidinsa.
T53: Shin umarnin waliyul fakih suna wajaba kan dukkan musulmai ne ko kuma wajibcinsa kawai kan masu yi masa takalidi ne? Kana shin wajibi ne ga wanda yake takalidi ga wanda bai yarda da wilayatul fakih na mutlaki ba ya yi biyayya ga waliyul fakih ko kuma a'a?
A: A bisa fikihun Shi'a wajibi ne ga kowane musulmi ya yi biyayya ga umarnin da suka fito daga waliyu amril muslimin, da kuma mika wuya ga umarni da hane-hanensa hatta ga sauran manyan malamai (maraji'ai) to ina ga masu yi musu takalidi! Mu ba ma ganin biyayya ga wilayatul fakih wani abu ne da yake da bambanci da yin biyayya ga addinin Musulunci da kuma jagoranci na lmamai ma'asumai (A.S)
T54: Hakika ana amfani da kalmar wilayatul mudlaka (iko na gaba daya) a zamanin Manzon Allah (sawa) da ma'anar cewa shi Annabi (sawa) idan da zai umarci wani mutum da aikata wani al'amari to wajibi ne ya aikata shi ko da kuwa alamarin yana daga lamurra mafi wahala, kamar da annabi (sawa) zai umurci wani mutum da ya kashe kansa to wajibi ne ya aikata hakan, to tambaya a nan ita ce: Shin "wilayatul mudlaka" har yanzu tana nan da wannan ma'ana? Tare da cewa shi annabi (sawa) ya kasance ma'asumi ne, amma a wannan zamani babu wani jagora ma'asumi?
A: Abin nufi da "wilayatul mudlaka" ga fakih (mujtahidi) wanda ya cika sharudda shi ne cewa shi addinin Musulunci - wanda shi ne cikamakin saukakkun addinai wanda kuma zai ci gaba da wanzuwa har zuwa ranar alkiyama - addini ne na hukunci da kuma jagorantar al'amurran al'umma, dan haka dole ne al'ummar musulmai da dukkan bangarorinsu su kasance suna da jagora mai mulkinsu (malami) kuma shugaba wanda zai kare su da addininsu daga abokan gabansu, kana ya kare musu tsarinsu, sannan ya tsayar da adalci a tsakaninsu, ya kuma hana masu karfi su zalunci masu rauni, ya kuma samar da abubuwan ci gaba na al'adu, siyasa da zamantakewarsu.
Watakila wajen gudanar da wannan al'amari ya yi karo da manufofin wasu ko bukatunsu ko burace-buracensu ko amfaninsu ko kuma ‘yancin wadansu mutane don haka wajibi ne ga jagoran musulmai yayin gudanar da al'amarin jagoranci bisa ga fikihun Musulunci da ya dauki matakai da suka dace idan ya ga bukatan hakan.
Kana dole ne ya zamanto ikonsa da kuma abin da ya yi nufin zartarwa ya zama shi ke da rinjaye kan iko da kuma nufin sauran jama'a a duk lokacin da wadannan manufofi guda biyu suka yi karo. To wannan dan takaitaccen bayani ne dangane da ma'anar ALWILAYAL MUTLAKA.
T55: Kamar yadda ci gaba da takalidin mamaci ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi bisa yadda fatawar malamai ta tafi akai, to shin umarni da hukunce -hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen jagoran da ya rasu su ma suna bukatan izinin sabon (rayayyen) jagora kafin su ci gaba da wanzuwa ko kuma a'a?
A: Hukunce-hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen "waliyi amril muslimin" da ya rasu in dai har ba na takaitaccen lokaci ba ne, to suna nan daram, sai dai idan sabon jagoran yana ganin akwai wata maslaha wajen shafe su, to yana da daman shafe su.
T56: Shin wajibi ne ga fakihin da yake zaune a jamhuriyar Musulunci ta lran idan har bai yarda da "wilayatul fakih"mudlaka ba - da ya yi biyayya ga umarnin waliyul fakih? To idan ya saba wa umarnin waliyul fakih shin za'a iya daukansa fasiki? Sannan idan wani fakihi ya kasance ya yarda da "wilayatul fakih" mudlaka, to amma yana ganin shi ya fi dacewa da wannan matsayi, to shin idan ya saba wa umarnin jagora da ke jagoranci ana iya daukansa a matsayin fasiki?
A: Wajibi ne ga kowane mukallafi, ko da kuwa mujtahidi ne, da ya yi biyayya ga hukunce-hukuncen jagoranci (hukuma) na waliy amril muslimin, ba ya halatta ga wani ya saba wa jagoran da yake jagoranci saboda da'awar cewa shi ya fi shi dacewa, hakan kuwa wajibi ne idan har shi jagoran da yake jagorancin ya hau wannan matsayin ne ta hanya da ta dace da dokokin da aka tsara domin haka, to amma in ba ta wannan yanayin ba, to al'amari ya bambanta.
T57: Shin mujtahidin da ya cika sharudda - a zamanin buya (gaiba) yana da ikon zartar da haddi?
A: Wajibi ne a gudanar da haddi a lokacin gaiba, ikon hakan kuwa yana hannun waliyi amril muslimin ne kawai.