BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
HUKUMCE-HUKUMCEN WANKAN DA BAI INGANTA BA
T124: Mutumin da ya kai shekarar balaga to amma sai ya kasance ya jahilci wajibcin wankan (janaba) da kuma yadda ake yinsa, sai bayan kimanin shekaru goma say a fahimci batun takalidi da kuma wajibcin wankan janaban. Mene hukumcin wannan mutumin? Sannan kuma mene ne hukumcinsa dangane da abin da ya shafi ramuwar salla da azumin da bai yi ba?
A: Ramakon sallar da ya yi su alhali yana cikin janaba wajibi ne. Haka nan azumin da ya yi alhali ya san yana da janaba sai dai kawai ya jahilci wajibcin yin wankan ne.
T125: Matashin da bayan shekaru sha hudu zuwa sama, saboda jahilci, ya kasance yana istimna'i da kuma fitar da maniyyi amma dai ban san cewa fitar maniyyi yana sanya wa mutum janaba ba sanann kuma wajibi ne ya yi wanka saboda salla da azumi, to a nan mene ne hukumcinsa? Shin wanka a lokacin da ya ke fitar da maniyyin ya hau kansa? Sannan kuma shin salla da azumin da ya yi har zuwa wancan lokacin ba su inganta ba kuma wajibi ne ya rama su?
A: Wanka guda daya ya wadatar ga fitar maniyyi na lokuta daban-daban matukar dai bai yi wanka ba, sannan kuma wajibi ne ya rama dukkanin sallar da ya yi alhali yana cikin janaban. Amma matukar a dararen watan Ramalana mutum ya jahilci asalin kasantuwarsa cikin janaban ne, to ba sai ya sake azuminsa ba, azuminsa ya inganta. Amma matukar ya san da batun fitar maniyyin da kuma kasantuwarsa cikin janaba, to amma bai san cewa wajibi ne ya yi wanka ba wajen ingancin azumin nasa, to a nan kan wajibi ne ya rama dukkanin azumin da ya sha alhali yana cikin janaba.
T126: Mutum ne ya samu janaba kana ya yi wanka, to amma wankan nasa bai yi shi dai-dai ba, to mene ne hukuncin sallar da ya yi bayan wankan, tare da cewa ya jahilci hakan?
A: Salla da wankan da ba'a yi dai-dai ba, ba ta inganta ba, wajibi ne a sake ta ko kuma a rama ta.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved