Snack's 1967
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali


HUKUNCE- HUKUNCEN TAIMAMA

Ali Khamenei4

T127: Idan abubuwan da ake yin taimama da su kamar turbaya, ko dutse da sauransu suka kasance a jikin gini ne, suke a damfare shin ya inganta a yi taimama da su ko kuma wajibi ne su kasance a kan kasa?

A: Kasantuwarsu a kan kasa ba sharadi ne na ingancin taimama da su ba.
T128: Idan na wayi gari cikin janaba kana ba zan iya yin wanka ba, har na ci gaba da kasantuwa cikin janabar na wasu ranaku, to shin wajibi ne kamar yadda ya kasance a baya in yi alwala ko kuma taimama ga duk wata sallar da zan yi bayan sallar da na yi mata taimama maimakon wanka, ko kuma ina iya takaita da sau guda kawai? Kana a irin wannan yanayi shin alwala ne ya wajaba ko kuma taimama ga kowace salla.

A: Da wani abin da ke bata alwala zai bijiro wa mai janaba bayan da ya yi sahihiyar taimama maimakon wankan janaba, to bisa ihtiyat sai ya yi taimama maimakon wanka kana ya yi alwala.
T129: Shin taimamar da aka yi ta maimakon wanka tana da hukuncin wanka ne? Wato shin zai iya aikata ayyukar da suka halatta ga wanda ya yi wanka ya aikata kamar shiga masallaci?

A: Duk wani aikin da ya halatta a aikata shi da wankan, yana ingantuwa a aikata shi da taimamar da aka yi ta maimakon wanka, sai dai ban da taimamar da aka yi ta maimakon wanka saboda kurewar lokaci.
T130: A wasu lokuta wani ruwa ya kan fita wa mutum yayin barci, to bayan farkawarsa ba zai iya tuna komai ba sai dai kawai ya ga tufafinsa jike, kuma ba shi da lokacin da zai tsaya don yin tunani saboda sallar asuba za ta tsere masa, to shin me ya kamata ya aikata a irin wannan hali? Shin zai yi niyyar taimama ne maimakon alwala ko kuma wanka? A takaice dai mene ne ainihin abin da ya wajaba a kansa?

A: Idan har ya san janaba ta samu a dalilin wannan mafarki to wanka ya wajaba a kansa, to amma saboda kurewar lokaci sai ya yi taimama bayan tsarkake jikinsa sannan daga baya ya yi wanka, to amma idan har yana shakkan mafarki da kuma janaba, to hukuncin janaba bai hau kan shi ba.
T131: Mutum ne ya yi salla da taimama saboda karancin lokaci, to amma bayan idar da sallar sai ya bayyana masa cewa ashe yana da lokacin da zai iya alwala, to mene ne hukuncin sallarsa?

A: Wajibi ne gare shi ya sake wannan salla.
T132: Muna raye ne a wani yanki da babu wurin da za'a yi wanka, to sai muka farka daga gabannin fitowar alfijir cikin janaba ga shi kuma cikin watan Ramalana ne, tattare da cewa mutane su ga saurayi yana wanka cikin dare da ruwan randa ko tanki babban aibi ne, kana kuma ga shi ruwan yana da tsananin sanyi, to mene ne abin yi dangane da azumin washe gari? Shin ya halatta mu yi taimama? Kana mene ne hukuncin karya azumin saboda rashin samun daman yin wankan?

A: A sabilin wahala ko kuma kasantuwan aikata wani aiki aibi ne a idon jama'a ba uzuri ba ne a fuskar shari'a face dai wajibi ne gare shi ya yi wanka ta duk yanayin da zai iya, matukar dai ba zai kasance da kunci ko cutarwa gare shi ba, to amma idan har akwai hakan to sai ya yi taimama, to zai yi taimama a wannan halin gabannin fitowar aifijir, kuma azuminsa ya inganta, in kuwa ya bari azumin ya baci, to amma duk da haka wajibi ne ya rike bakinsa har zuwa faduwar rana.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din