Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUNCE- HUKUNCEN MATA
Ali Khamenei4

T133: Mene ne hukuncin dan ruwa-ruwan da mace ta ke gani bayan tana da yakinin ta samu tsarki, tattare da cewa ba shi da wani siffa na jini ko kuma jinin da ya hadu da ruwa?

A: Idan har ba jini ba ne to ba shi da hukuncin haila, banbance wannan al'amari kuwa yana hannun macen ne.
T134: Mene ne hukuncin hana yin haila ta hanyar shan magunguna don saboda samun daman yin azumi?

A: Ba wata matsala ga hakan.
T135: Idan mace ta sami matsalar zuban jini yayin da ta ke da ciki, ko da yake cikin bai zube ba, to shin wanka ya wajaba gare ta ko a'a? A takaice dai mene ne ya wajaba gare ta ta aikata?

A: Jinin da mace ta gan shi yayin da take da ciki idan yana da siffofi ko kuma sharuddan haila, to haila ne, in kuwa ba haka ba to istihala ne, idan har istihala mai yawa (kasira) ne ko kuma matsakaici (mutawassida) ne to wajibi ne ta yi wanka.
T136: Macen da ta ke da takamammen al'ada misali kwana bakwai, to sai daga baya ta fara ganin jini har na tsawon kwanaki goma sha biyu saboda amfani da bututun hana ciki, to shin wannan jini da ya karu akan kwanaki bakwai haila ne ko istihala?

A: Idan har jini ya wuce kwanaki goma, to dai-dai kwanakin hailanta shi ne haila sauran kuma istihala ne.
T137: Shin macen da ta yi bari ko kuma aka mata aikin zubar da ciki, ta zama mace mai jinin haihuwa ne ko kuma?

A: Idan har bayan faduwar jaririn - ko da kuwa gudan jini ne - ta ga jini to ana daukan ta a matsayin mai jinin haihuwa ne.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog