Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali


HUKUNCE- HUKUNCEN MAMACI

Ali Khamenei4

T137: Shin taba kashin da yake da nama a jikinsa da aka cire ko ya fita daga jikin mutum rayayye, yana wajabta wankan taba jikin mamaci?

A: Na'am a wannan yanayi da aka ambata yana wajabta wanka.
T138: Yayin cire hakori ya kan fita tare da wani bangare na dasashin mutum, to shin taba wannan dasashin yana wajabta wankan taba mamaci?

A: A'a ba ya wajabta wankan.
T139: Ni dalibi ne na jami'a a bangaren likitanci, to a wasu lokuta ya kan zama dole mu taba jikin mamata yayin darasi, tare da cewa ba mu san wadannan mamata musulmai ne ko kuma a'a ba? To amma shuwagabannin gurin su kan ce mana an riga an yi wanka wa wadannan mamata, dan haka muke so a mana bayani kan abin da ya wajaba a kan mu dangane da salla da dai sauransu bayan taba wadannan gawawwaki kana bisa ga abin da aka ambata shin wajibi ne sai mun yi wanka?

A: Idan har asalin yin wanka ga wadannan mamata bai bayyana maka ba kana kuma kana da shakkan faruwar hakan, to wajibi ne ka yi wankan shafan mamaci idan har ka taba su ko wani bangare na jikinsu kana salla ba ta inganta in har ba ka yi wanka ba. To amma idan har ya bayyana maka cewa an yi musu wanka to babu wata matsala idan ka shafi jikin nasu ko kuma wani bangare na jikin ko da kuwa kana shakkan ingancin wankan.
T140: Idan wani mutun ya fara rurrushe makabartan musulmai ba tare da la'akari da abin da shari'a ta shinfida ba, to mene ne abin da ya wajaba kan sauran musulmai dangane da wannan mutum?

A: Abin da ya wajaba kansu shi ne hana faruwar mummunan aiki amma tare da la'akari da sharudda da kuma martabobinsa.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din