Pair of Vintage Old School Fru
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

NAJASOSI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENSU
Ali Khamenei4

T141: Shin jini yana da tsarki?

A: Jinin dabban da jininta yake gudanya yayin yanka shin dan'Adam ne ko kuma waninsa najasa ne.
T142: Alamar jini da yake saura a jikin tufafin mutum bayan wanke shi, shin najasa ne?

A: Idan dai har abin da ya saura din ba ainihin jinin ba ne, kana kuma ya ki fita bayan an wanke shi, to ba najasa ba ne.
T143: Mene ne hukuncin gudan jinin da ke cikin kwai?

A: Ba najasa ba ne amma cin sa ya haramta.
T144: Mene ne hukuncin gumin mai janaba ta hanyar haram da kuma gumin dabban da take cin najasa?

A: Gumin rakumin da yake cin najasa, najasa ne, to amma gumin sauran dabbobin da suke cin najasa in ban da rakumi, haka ma kuma gumin mai janaba ta hanyar haram ba najasa ba ne a bisa magana mai karfi, to amma lhtiyat na wajibi shi ne kada a yi salla tare da gumin janaba ta hanyar haram.
T145: Malamai a cikin littafan fikihu sun nuna cewan kashin dabbobi da kuma tsuntsayen da cin namansu bai halatta ba najasa ne, to shin kashin dabbobin da ake cin namansu, kamar shanu, tumaki da kaji najasa ne ko kuma a'a?

A: Kashin dabbobin da cin namansu ya halatta ba najasa ba ne.
T146: Idan bako ya najasta daya daga cikin kayayyakin gidan mai masaukinsa, shin wajibi ne ya sanar da mai gidan?

A: Ba wajibi ba ne ya sanar da shi sai dai in abinci ne ko abin sha ko kuma kwanukan cin abinci.
T147: Shin abin da ya shafi wani abin da ya najastu yana najastuwa? To idan yana najastuwa, shin hakan ya shafi dukkan abubuwan da suka shafe shi ne daya bayan daya ko kuma kawai ya takaita ga na kurkusa ne?

A: Abin da ya shafi najasa yana najastuwa haka ma abin da ya shafe shi, kana abin da ya shafi na biyun ma bisa lhtiyat shi ma yana najastuwa, to amma abin da ya shafi na ukun ba ya najastuwa.
T148: Idan mutum ya yi amfani da takalmin da aka yi shi da fatar dabbar da ba'a yanka ta ba (kamar yadda Musulunci ya tsara), to shin wajibi ne gare shi da ya wanke kafarsa duk lokacin da zai yi alwala kasantuwar a wasu lokuta kafar tasa ta kan yi gumi?

A: Idan har ya tabbatar da cewa kafar tasa ta yi gumi a cikin irin wannan takalmi, to wajibi ne ya tsarkake ta.
T149: Mene ne hukuncin tufafin da ake ba da su ga masu wanki dan wankewa kasantuwa sauran wasu mutanen da ba musulmai ba su ma suna kawo wankin kayayyakinsu tattare da cewa su masu wankin suna amfani da wasu magunguna wajen wankin?

A: Tufafin da ake ba wa masu wanki idan har ba daman can suna da najasa ba ne to masu tsarki ne, haduwar tufafi da tufafin mabiya sauran addinai na daga cikin Ahlul- kitab ba ya najastar da su.
T150: Shin ruwan da ke zuba akan titi ta hanyar motocin diban shara idan ya fantsamu a jikin mutum, shin wannan ruwa ana hukunta shi da abu ne mai tsarki ko kuma mai najasa?

A: Abu ne mai tsarki sai dai idan mutum ya samu yakini kan cewa ruwan ya najastu ta hanyar haduwa da najasa.
T151: Shin ruwan da ke taruwa a cikin ‘an ramukan da suke kan tituna mai tsarki ne ko kuma najasa ne?

A: Wannan ruwa mai tsarki ne.
T152: Mutum ne ya ke sai da abinci kana kuma yana amfani da hannunsa da ke da jika wajen hakan tattare da cewa ba'a san shi mabiyin wani addini ba ne, to shin wajibi ne a tambaye shi addininsa ko kuma ana iya gudanar masa da hukuncin tsarki (wato ko wani abu mai tsarki ne har sai in najastuwansa ya bayyana)? Tare da cewa shi ba daga garin musulmai ya ke ba.

A: Tambaya kan addininsa ba wajibi ba ne, ana iya gudanar da hukuncin tsarki gare shi da kuma abin da ya taba da jikinsa da ke da jika.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din