T153: A wannan zamani namu ana amfani da alkwan "alkohol" wajen yin da yawa daga cikin magunguna (musamman magungunan da ake sha) da kuma turare, shin ya halatta ga mutumin da ya san hakan ko kuma wanda ma bai sani ba da ya sayar ko ya saya ko kuma ya yi amfani da wadannan abubuwa?
A: "Alkohol" din da ba'a tabbatar da kasantuwarsa ruwa ba ne tun asali to shi yana da tsarki ko da kuwa yana sa maye, babu wata matsala wajen amfani da shi wajen magani da sauransu, kamar yadda babu laifi wajen salla da tufafin da wannan alkwan "akohol" ya taba.
T154: Mene ne ake lura da shi wajen najastuwan "alkohol"? Kana wasu hanyoyi ne ake bi wajen tabbatar da abin sha yana sa maye?
A: Abin da ake lura da shi ya kasance yana sa maye kana kuma ya kasance asalinsa ruwa ne. Sannan hanyar da ake bi ita ce ta hanyar ba da labarin wadanda suka san kan al'amarin idan har shi mukallafi bai da yakini a kan haka.
T155: Mene ne hukuncin shan lemunan kwalban da ake sayarwa a kasuwa (kamar su Coca-Cola, pepsi.....) tattare da akan ce ainihin abubuwa da ake yin su da su daga waje ake shigowa da su, kana kuma akwai yiyuwan cewa sun kunshi "alkohol"?
A: Masu tsarki ne kuma sun halatta a sha, sai dai idan shi mukallafi yana da yakinin cewa sun kunshi "alkohol" mai sa maye wanda asalinsa ruwa ne.
T156: Yayin sayen kayayyakin abinci (musamman na gwangwani) shin wajibi ne a nemi sanin cewa sun kunshi "alkohol" ko kuma sun taba hannun wanda ya yi su ko kuma ba wajibi ba ne?