T157: Ni na kasance tsawon shekaru an jarrabe ni da bala'in waswasi, hakika wannan al'amari sai gaba-gaba ya ke yi har ya zamanto ina samun shakku cikin kowani abu ta yadda rayuwata ta kasance cikin shakku, kuma mafi yawan shakkun nawa kan abinci ne da kuma abubuwan da suke da jika a jikinsu, dan haka na kasance ba na iya gudanar da rayuwa kamar sauran mutane. Domin a duk lokacin da zan shiga wani guri sai na cire safa ta don ina tunanin cewa watakila safan tawa ta jike da gumin cikin takalmi ta yadda za su iya najastuwa idan suka taba najasa. Kana kuma ba na iya zama a kan darduma, kai idan har ma na zauna to na dinga juye-juye kenan wai don kada in dauki gashin darduman a jikin rigata ta yadda zai zama dole in wanke ta da ruwa, ko da yake da ba haka nake ba, to amma wannan abu ya dame ni sosai, ta yadda a ko da yaushe na kan so da wata mu'ujiza za ta zo ta tsamo ni daga wannan matsala in koma kamar yadda nake da. Don haka na ke bukatan ka shiryar da ni kan abin da ya dace?
A: Hukunce- hukuncen tsarki da najasa su ne dai wadannan da aka riga aka yi bayaninsu cikin littattafan fikihu, a sharia kowani abu mai tsarki ne sai dai abin da sharia ta nuna cewa shi najasa ne, kuma najastuwansa ya tabbata ga mutum ta hanyar yakini. Dan haka fita daga waswasi ko shakku ba ya bukatuwa ga wata mu'ujiza, face dai kawai wajibi ne mutum ya ajiye tunace-tunacen radin kansa a gefe ya yi riko ya kuma yi imani da karantarwar shari'ar Musulunci, ya yi aiki da shi kada ya dauki wani abin da bai da yakini kan najastuwansa a matsayin najasa. Daga ina kika sami yakinin cewa kofa, garu ko darduma da sauran abubuwan da kike amfani da su najasa ne? Yaya aka yi kika sami yakinin cewa gashin dardumar da kike tafiya akai ko kuma kike zama akai najasa ne? Har ma kike ganin cewa najasar su zata komo ga safa, ko tufafi ko kuma jikinki? To ko ma dai yaya ne, ba ya halatta gare ki, ki kula da wannan waswasi naki, dan haka rashin kulawa da wannan waswasi da kuma gwada rashin kulawan lalle zai taimake ki (lnsha Allah) wajen kubutar da kanki daga bala'in waswasi.