NAJASAR KAFIRI TSARKIN AHLUL-KITAB DA HUKUMCIN SAURAN KAFIRAI
T158: Wasu malaman suna ganin cewa su Ahlul kitab ba najasa ba ne, to mene ne fatawarka kan su Ahlul kitab?
A: Najasar zatin Ahlul -kitab bai bayyana ba, face dai mu muna ganin su masu tsarki ne a zatinsu.
T159: Ni da wasu daga cikin abokaina mun dauki hayar gida, to amma sai na gano cewa daya daga cikinsu ba ya salla, ko da muka bukaci karin bayani daga wajensa, sai ya amsa mana da cewa shi dai ya yi imani da Allah amma dai salla ce kawai ba ya yi, to bisa la'akari da cewa muna cin abinci da kuma sauran mu'amaloli tare, to shin shi najasa ne ko kuma a'a?
A: Dan barin salla ko azumi da kuma sauran wajiban shari'a ba ya tabbatar da riddan musulmi, ko najasarsa matukar dai ba a tabbatar da cewa ya yi ridda ba to hukuncinsa kamar sauran musulmai ne.
T160: Mene ne ake nufi da Ahlul-Kitab? kana mene ne abin lura wajen iyakance yin mu'amala da su?
A: Abin da ake nufi da Ahlul- Kitab shi ne duk wani wanda ya riki addini na Allah kana kuma yake ganin kansa daga cikin al'ummar wani Annabi daga cikin Annabawan Allah (tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabinmu da mutanen gidansa da kuma gare su) kana kuma ya kasance suna da wani littafi daga cikin littattafan sama wanda aka saukar wa Annabawa (a.s), kamar Yahudawa, nasara, zorostawa da kuma sabi'awa domin kuwa duk wadannan - kamar yadda muka yi tahkiki - suna daga cikin Ahlul-kitabi don haka hukuncin wadannan hukuncin Ahlul kitab ne, mu'amala da su tare da kulawa da tsari - da kuma dabi'u na Musulunci babu matsala a cikinta.
T61: Akwai wata kungiya da take ganin Amirul muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ubangiji ne kana sun yi imani da karanta addu'oi maimakon yin salla, da azumi to shin wadannan najasa ne?
A: Idan har sun yi imani da cewa Amirul muminin(a.s) (ubangiji ne), Allah ya tsare mu da haka, to hukuncinsu kamar hukuncin sauran wadanda ba musulmai ba ne amma banda Ahlul-kitab.
T162: Shin ya halatta ga 'yan Shi'a isna Ashariyya su bayar da abubuwan da aka yi bakance ga lmam Hussain (a.s) ko kuma ga sauran Ahlul, Baiti (a.s) su bayar da su zuwa ga wasu cibiyoyin mutanen da suke ganin lmam Aliyu (a.s) a matsayin ubangiji wanda hakan zai iya zama taimako ne wajen raya wadannan cibiyoyi?
A: Imani da Allantakan shugaban masu tauhidi Aliyu bn Abi Talib (A.s) batacciyar akida ce, da take fitar da duk wani ma'abucinta daga Musulunci, hakika taimakawa wajen yada wannan batacciyar akida haramun ne, kana kuma sarrafa dukiyar bakance ba ya halatta ga abin da ba dan shi a ka yi bakance ba.
T163: Mafi yawan mutanen garinmu kafirai ne, lokacin da wani kamar dalibin jami'a ya kama hayan gida a gurin, to yaya zai yi da najasar da ke gidan? shin dole ne ya wanke ya kuma tsarkake gidan ko kuma a'a? Yana da kyau a sani cewa yawancin gidajen da katako aka yi su inda wanke su ba zai yiwu ba, kana mene ne hukuncin kujeru da sauran kayayyakin gidan ko kuma guraren saukan baki a garin?
A: Matukar dai ba'a tabbatar da shafuwan jikaken hannu ko jikin kafiri wanda ba Ahlul-kitabi ba, ba za'a hukunta shi da najastuwa ba, to ko da ma an tabbatar da najasar ba wajibi ba ne a tsarkake kofofi da kuma garun gidan, haka ma kujeru da sauran kayayyakin gidan, da wurin saukan baki face dai abin da yake wajibi shi ne tsarkake abubuwan da suka najastu na daga abubuwan da ake amfani da su wajen ci da sha da kuma salla.
T164: Mene ne hukuncin aiki a gurin yahudawa da sauran kungiyoyin kafirai, da kuma karban albashi a wajensu?
A: Shi kansa aikin babu matsala tare da shi matukar dai aikin ba yana cikin al'amurran da suka haramta ba ne ko kuma suka saba wa maslahohin Musulunci da musulmai na gaba daya ba.
T165: Mene ne hukuncin kujerun motoci da jiragen kasa wanda musulmai da kafirai suke amfani da shi dukkansu tattare da cewa a wasu wuraren kafiran sun fi musulman yawa, shin za'a yi musu hukunci da tsarki ne, tattare da cewa zafin da ke gurin ya kan sa yin gumi da kuma zubansa?
A: Idan dai har ba'a tabbatar da najasar ba, to ana musu hukunci da tsarki ne.
T166: Mutumin da ya yi inkarin wasu bayyanannun lamurra na addini kamar salla, azumi da dai sauransu, shin hukuncin kafiri ya hau kansa ne ko kuma a'a?.
A: Idan har inkarin nasa ya jawo inkarin sakon Manzon Allah (sawa) ko kuma karyata shi Manzon Muhammad ko kuma ya jawo rashin daraja ga shari'a, to ya kafirta ya kuma bar Musulunci.