BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Bukatu
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
" ﺍﻟﺤﻮﺍﺋﺞُ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠّﻪ ﻭﺃﺳﺒﺎﺑﻬﺎ
ﻓَﺎﻃْﻠُﺒﻮﻫﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠّﻪ ﺑﻬﻢ ﻓﻤﻦ
ﺃﻋﻄﺎﻛﻤﻮﻫﺎ ﻓﺨﺬﻭﻫﺎ ﻋﻦ ﺍﻟﻠّﻪ
ﺑﺼﯿﺮ "
"Biyan bukatu a wajen Allah
ta hanyar sabubbanta ne,
don haka ku neme su daga
wajen Allah ta hanyarsu.
Abin da suka baku, to ku
karbe shi a madadin Allah
da hakuri".
(Tuhaful-Ukul shafi na 48).
A wannan hadisi an yi
cikakken bayani ne
dangane da matsayin
sanadi da dalili na dabi'a
dangane da bukatun
mutum. Kalmar ﺑـﻬـﻢ" "
wakilin suna ne na jam'i
dake nufin masu hankali,
wanda yake nuni da cewa
da dama daga sanadin
biyan bukatunmu suna
zuwa ne ta hanyar mutane.
To sai dai duk da cewa
mutum yana samun biyan
bukatunsa ne ta hanyar
dalilai na dabi'a (wanda a
mafi yawan lokuta su ne
mutane) sai dai duk da
hakan dole ne mutum ya
dinga kallon Ubangiji tare
da jin cewa Shi ne
mamallakin dukkan komai
(wato komai daga wajensa
yake).
Saboda haka neman biyan
bukata ta hanyar sanadi ba
tare da neman taimakon
Allah ba, kokari ne tauyayye,
haka nan komawa ga
masallaci domin rokon Allah
biyan bukata ba tare da yin
riko da sanadi ba, shi ma
kokari ne tauyayye. Don
haka dole ne a hada
dukkanin hanyoyin biyu
domin kai wa ga biyan
bukatu tare da juriya da
hakuri.