T627: "Haddut tarakkhus: Shi ne daga inda mutum ya daina jin kiran sallar garin da ya fito kana da kuma buyan ganuwar garin, to shin wajibi ne sai wadannan abubuwa biyu sun kasance ko kuma guda ma daga cikinsu yana wadatarwa?
A: Ihtiyati shi ne lura da dukkansu, ko da yake rashin jin kiran salla ma yana wadatarwa.
T628: Shin abin lura wajen gane "haddut tarakkhus" shin jin kiran sallar gidajen farko da suke farkon gari ne ko kuma masallatan tsakiyan gari?
A: Ma' aunin dai shi ne kiran sallar gidajen karshe na garin daga ta wajen da matafiyi zai bar garin ko kuma zai shigo.
T629: An sami sabani tsakanin wasu jama' a: Wasu suna cewa abin lura dangane da "haddut tarakkhus" shi ne gidajen karshe na garin, wasu kuma suna cewa a'a abin lura shi ne kamfanoni da masana'antu da suke bayan garin, to tambaya a nan ita ce, yaya ake gane karshen gari?