T630: Ni na kasance an haife ni ne a wani gari misali garin Bauchi kana kuma mahaifana mutanen Kaduna ne misali, dan haka a kowace shekara su kan je Kaduna sau da yawa to ni ma na kasance ina tafiyar tare da su, to mene ne hukuncin sallata? Tattare da cewa ni ba ni da niyyar komawa wannan gari na iyayena don zama a garin, ni dai zan ci gaba da zama ne a wannan gari na Bauchi.
A: Bisa ga wannan yanayi da ka ambata, hukuncin sallar ka da azuminka a wannan gari na mahaifanka shi ne hukuncin salla da azumin matafiyi (wato kasaru za ka yi).
T631: Ni na kasance a cikin shekara na kan zauna a wani gari na wata shida, kana kuma wata shida a wani gari na daban wanda shi ne inda nake zaune da kuma iyalaina, to amma zama na a wannan garin na farko ba a jere ba ne a wasu lokuta na kan zauna a gurin ne na tsawon sati biyu ko kuma kwana goma ko kuma kasa da haka, sannan sai in koma wannan gari wanda ni da iyalaina muke da zama a ciki, to tambaya a nan ita ce yayin da na yi niyyar zama a wannan gari na farko na kwanaki kasa da goma, to shin hukuncina hukuncin matafiyi ne ko kuma a'a?
A: Idan har wannan gari ba garinku ba ne kuma ba ka da niyyar mayar da shi ya zama garinka, to hukuncinka a duk lokacin da ba za ka zauna na kwanaki goma ko fiye a gurin ba hukuncin matafiyi ba ne.
T632: Shin hukuncin garin da mutum yake aiki a ciki dai-dai yake da hukuncin garinsu?
A: Yin aiki a guri ba ya mayar da gurin ya zama garin mutum, to amma da a duk kwanaki goma zai tafi wurin wannan aiki nasa sau guda alal akalla idan har ratan wurin aikin nasa daga garin da yake da zama ya kai nisan da shari'a ta yarda da shi wajen yin kasaru, to zai cika sallarsa ne kana kuma azuminsa ya inganta a wannan gurin aiki nasa.
T633: Muna so ka yi mana bayani kan mas'alar garin asali da kuma gari na biyu?
A: Garin asali: Shi ne wurin da aka haifi mutum, kana ya girma a gurin. Gari Na biyu kuwa: Shi ne wurin da mutum ya zaba don ya rayu a gurin na dindindin ko da kuwa na tsawon wasu watanni ne a kowace shekara.
T634: Shin ana daukan garin da aka haifi mutum a ciki a matsayin garinsa ko da kuwa bai zauna a garin ba?
A: Idan har ya zauna a garin na wani lokaci kana kuma a garin ya girma, to matukar dai bai canza gari ba to garin yana da hukuncin garinsa ne, idan kuwa ba haka ba to bai kasance garinsa ba.