Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

SALLAR AYOYI
Ali Khamenei4

T635: Me ake nufi da "Salatul Ayat" (sallar ayoyi) kana kuma wasu abubuwa ne suke wajabta ta a shar'ance?

A: Ita salla ce mai raka'a biyu wacce kowace raka'a tana da ruku'u biyar da sujada guda biyu. Abubuwan da suke wajabta ta kuwa a shar'ance su ne rashin lafiyar rana ko wata (wato husufin rana ko wata) ko da kuwa wani sashe ne nasu, da girgizar kasa da kuma duk wani abin da ya tsorata mafi yawan mutane, kamar baka ko jan guguwa wanda ta saba wa yadda aka saba ganin guguwa, da kuma tsananin duhu, da tsawa mai tsananin gaske, da wuta wanda kan baiyana a sama, dukkan wadannan abubuwa in ban da husufin wata da rana da kuma girgizan kasa to sallar ba ta wajaba har sai idan sun kasance abin tsoratarwa ga mafi yawan jama'a.
T636: Yaya ake yin 'Salatul Ayat.

A: Tana da yanayi dadan- daban: Yanayi na farko: Shi ne bayan niyya da kabbarar harama sai ya karanta fatiha da sura sai ya yi ruku'u kana sai ya dago ya sake karanta fatiha da sura ya yi ruku'u ya daga, ya sake karanta fatiha da sura ya yi ruku'u ya daga, haka dai zai ta yi har ya cika ruku'u na biyar daga nan sai ya tafi zuwa sujada ya yi sujada guda biyu kana ya taso ya kawo raka'a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, daga nan sai ya yi tahiya ya yi sallama.

Yanayi na biyu: Bayan niyya da kabbarar harama sai ya karanta fatiha da wata aya ta cikin wata sura (misali suratul Tauhid) sai ya yi ruku'u, sannan ya dago ya karanta wata aya kuma ta wannan surar ya yi ruku'a, sannan ya dago ya karanta wata aya ta wannan sura ya yi ruku'u, haka dai zai ci gaba da yi har ya kai ga ruku'u na biyar da ayar karshe na wannan sura, daga nan sai ya yi sujada guda biyu kana ya taso ya kawo raka'a ta biyu kamar yadda ya yi ta farko, kana sai ya yi tahiya ya yi sallama. To amma a irin wannan yanayi fatiha guda kawai zai karanta a kowace raka'a.
Yanayi na uku: Shi ne ya yi raka'a ta farko a daya daga cikin wadannan yanayi da aka ambata a sama kana a raka'a ta biyu kuwa ya yi daya yanayin.

Yanayi na hudu: Shi ne ya cika surar da ya riga ya karanta farkonta tun a tsayuwarsa ta farko to sai ya cika ta a tsayuwansa na biyu ko na uku ko na hudu, to a nan wajibi ne gare shi bayan dagowa daga ruku'u ya sake karanta fatiha a tsayuwar da za ta biyo baya kana kuma ya karanta sura ko kuma wata aya na wata sura. To amma idan kafin tsayuwa ta biyar aya ce ya karanta daga wata sura a tsayuwa ta hudu to wajibi ne ya cika waccan surar kafin ya yi ruku'u na biyar.

T637: Shin wajibcin salatul ayat ta ta'allaka ne ga mutumin da ke garin da wannan al'amarin ya faru ne? Ko kuma ya hada da dukkan wani baligin da yake da masaniya wajen faruwarsa ko da kuwa ba a garin yake ba?
A: Wajibcin nata ya ta'allaka ne ga mutumin da ke garin da abin ya faru, hakan kuwa ya hada har da mutanen da suke hade da garin da wannan abu ya faru idan dai har ana ganinsu kamar gari guda ne.
T638: Shin mutumin da a lokacin da ake girgizar kasa ya kasance ba a cikin hankalinsa (ya kasance cikin yanayi na suma) ba sai bayan da aka gama ne ya dawo cikin hankalin nasa. To shin wajibi ne ya yi sallar aya?

A: Matukar bai san girgizar kasar ta faru ba har sai bayan da aka gama ta gaba daya, to yin sallar aya a gare shi ba wajibi ba ne. Ko da yake bisa ihtiyati an so ya yi sallar.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din