KAN ABUBUWAN DA KHUMSI YA WAJABA AKANSU KYAUTA, SADAKI DA KUMA GADO
T824: Shin akwai "Khumsi" a cikin abin da aka ba wa mutum kyautarsa ko taimakonsa ko kuma a'a?
A: Babu "Khumsi" a cikin kyauta ko taimako, ko da yake a bisa ihtiyati ne a cire khumsin abin da ya saura daga cikinsu bayan bukatunsa na cikin shekara.
T825: Shin Khumsi yana hawa kan kyautar da banki yake bayarwa ga mutane (masu mu'amala da su) ko kuma a'a?
A: Ba wajibi ba ne a cire Khumusi cikin kyauta.
T825: Shin ana lissafa abin ciyarwar da mahaifi, ko dan'uwa ko daya daga cikin dangi ke bayarwa ga mutum a matsayin kyauta ne ko kuma? To idan shi mai bayarwan ba ya cire khumsin dukiyarsa, shin wajibi ne ga wanda aka ba shi din da ya cire khumsinsa?
A: Tabbatuwar kyauta ko taimako ya ta'allaka ne da niyyar mai bayarwar, kana matukar dai bai ga yakinin ta'allakan khumsi da abin da aka ba shi, ba to ba wajibi ba ne ya cire khumsinsa.
T826: A cikin littafin "Tahrirul wasila" an ambaci cewa khumsi ba ya ta'allaka da kudin sadaki. To amma ba‘a ambaci cewa sadakin da aka bayar ne gare ta (lakadan) ko kuma wanda take bin bashinsa ba (ajalan). Don haka muke son karin bayani.
A: Babu wani bambanci shin sadakin an riga an karba ne ko kuma ana bin bashinsa, haka nan ba bambanci shin kudi ne ko kuma kadara.
T827: Shin khumusi yana hawa kudin albashina da na ke Tarawa don sayen kayayyakin da nake bukata wajen aure a nan gaba?
A: Idan har shi kansa kudin albashin ne ka ajiye, to wajibi ne idan shekarar khumusinka ta yi ka fitar da khumusin. Sai dai idan har kana so ka sayi kayayyakin bukata na auren ne cikin watanni biyu zuwa uku sannan kuma idan har ka cire khumusin ba za ka samu damar saye ba.
T828: Shin khumsi ya ta'allaka da irin kudin nan da ma'aikatar ilmi take ba wa dalibai (sukolashif) don saukaka musu alamurran karatunsu?
A: Babu khumsi a cikin taimakon da ake bayarwa dan saukaka al'amurran karatu.