80s toys - Atari. I still have
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

BASHI, ALBASHI, INSHORA DA KUMA FANSHO
Ali Khamenei4

T830: Idan mutum ya karbi bashin kudi, to sai bai samu biyan bashin ba gabanni shekaran khumsinsa, shin khumsin dukiyar tana kan wanda ya karbi bashin ne ko kuma wanda ya bayar?

A: Babu khumsi ga kudin bashin akan wanda ya karbi bashin, to amma wanda ya bayar, idan har abin da ya bayar din daga cikin riban kasuwancinsa ne kuma bai riga ya cire masa khumsi ba, to idan har zai iya karban dukiyar tasa daga hannun wanda ya ba da bashin gare shi kafin cikan shekaran khumsinsa, to a wannan hali wajibi ne ya fitar da khumsinsa, idan kuwa ba zai iya karba ba har cikan shekaransa to a wannan hali khumusinsa bai wajaba a kansa ba a yanzu haka sai dai kawai ya jira lokacin da za a dawo masa da dukiyar, idan aka dawo da shi to a yayin nan wajibi ne a yi khumusinsa.

T831: Mutanen da suke karban kudin fansho shin wajibi ne su fitar da khumsin albashin da suke karba a shekara?
A: Albashin da ma'aikata suke karba bayan barin aikinsu idan daga cikin abin da ake yankewa daga cikin albashin su yayin da suke aiki ne kana a basu bayan sun yi ritaya, to idan har ya wuce abin da suke bukatuwa da shi na shekara da ya karba to wajibi ne su fitar masa da khumsi.

T832: Albashin ma'aikatan da hukuma ta jinkirta ba su tun shekaru, to shin yayin da ya karbe su za'a kidanya su ne a matsayin riban wannan shekarar (wato shekarar da ya karba) ta yadda khumsinsa zai kasance a dai-dai lokacin da shekaransa ta cika, ko kuma shin tun asali ma khumsi bai ta'allaka da wannan dukiya ba?
A: Zai lissafa ta ne daga cikin riban shekarar da ya karbe ta kana kuma khumsi ta hau kansa idan har ta wuce bukatunsa na shekara.

T833: Shin khumsi yana wajaba akan kudin da kamfanonin inshora suke bayarwa ga masu alaka da su kan asarorin da suka shafe su?

A: Babu khumsi ga kudin da kamfanonin inshora suke bayarwa ga mutanen da suke da alaka da su.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din