BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
DUKIYAR DA AKA TONO DA KUMA HALAL DIN DA YA HADU DA HARAM
T834: Mene ne fatawarka dangane da dukiyar tsintuwa da mutane suka tono a cikin kasar da mallakarsu ce?
A: Idan har ba ya tsammanin cewa dukiyar ta tsohon mai gurin ne, to ta wanda ya samo ta ne kuma a wannan hali khumsi ya hau kansa idan ta kai dinare ashirin na zinare ko kuma dirhami dari biyu na azurfa. A abin da kuma ba zinare ko azurfa ba ne shi ma wajibi ne a fitar da khumusinsa idan ya kai kimar yawan zinare ko azurfa da muka ambata, idan har hukuma ko wani ba su hana shi mallakarta ba, amma idan suka hana shi ko kuma suka kwace abin da ya samo din, to idan har akwai wani abin da ya saura a hannunsa kana kuma ya kai nisabi, to wajibi ne ya cire masa khumsi, to idan kuwa ba haka ba ne to babu khumsi a gare shi.
T835: Da dukiyar haramun za ta shiga dukiyar mutum, to mene ne hukuncin wannan dukiyar, kana yaya za ta iya halatta? Sannan kuma mene ne ya wajaba a gare shi ya aikata idan yana da ilimi kan haramcinsa ko kuma bai da shi?
A: Idan har yana da yakinin samuwar dukiyar haramun a cikin dukiyarsa, to amma bai san daidai yawanta ba kana kuma bai san mai ita ba, to hanyar tsarkake ta ita ce fitar da khumsinta, to amma idan har shakkan haduwan nata da ta haramun din yake yi to babu komai a gare shi.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved