Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

ABUBUWAN BUKATA (NA YAU DA KULLUM)
Ali Khamenei4

T836: Shin khumsi yana hawa kan irin zinaren da miji yake saya wa matarsa ko kuma?

A: Idan har yawansa bai wuce na abin da aka saba wanda ya dace da halinsa ba to babu khumsi a cikinsa.
T837: Idan mutum yana da wani fili na biyu da ya yi dai-dai da irin yanayinsa, kana kuma yana da bukatarsa dan shi ma'abucin iyalai ne, kana kuma bai samu daman gina filin ba a cikin shekaran khumsinsa, ko kuma bai iya gama gina shi a cikin shekara guda ba, to shin khumsi ya hau kansa?

A: Babu bambanci wajen rashin wajabcin khumsi tsakanin fili guda daya da kuma filaye da yawa, kana kuma tsakanin matsuguni guda ko kuma da yawa abin lura dai shi ne bukatuwansa gare shi gwargwadon yanayinsa da kuma yanayin tattalin arzikinsa wajen ginin a hankali a hankali.
T838: Idan mutum bai yi amfani da kayayyakin girki da cin abinci na gida ba ko kuma bai yi aiki da darduman salla ba har na tsawon shekara guda, ko da yake yana bukatuwa da su wajen hidima ga baki (idan suka zo), to shin khumsi ya hau kansu?

A: Babu khumsi a kansu.
T839: Bisa la'akari da fatawar lmam Khumaini (r.a) kan mas'alar kayayyakin gida da amarya take tafiya da shi zuwa gidan mijinta, to idan a wata al'ummar ya kasance shi mijin ne ko kuma iyayensa ne za su tanadar da wadannan kayayyaki, to dan haka sai suka fara sayen kayayyakin a hankali a hankali har shekara ta zagayo, to shin mene ne hukuncin wadannan kayayyaki?

A: Idan har wannan tari da suke yi na wadannan kayayyaki dan saboda gaba ana iya kirga shi a matsayin abubuwan da suke bukata kuma ba su da wata hanyar da za su same shi sai ta wannan hanya ta tari, to babu khumsi a cikinsu.
T840: Yaya ake lisafin khumsin kayayyakin gida?

A: Kayayyakin da za'a iya amfani da su a dai-dai lokacin da kuma asalinsu yana nan kamar darduma da dai sauransu babu khumsi a cikinsu, amma kayayyaki masu karewa kamar su shinkafa man gyada da wasunsu to duk abin da ya wuce har ya kai dai-dai shekara, to za'a fitar da khumsinsa.
T841: A wasu lokuta a kan sayar mana da wasu kayayyakin gida kamar firinji da araha kasa da yadda ake sayarwa a kasuwa, to kuma wadannan kayayyaki dole ne mu neme su a nan gaba yayin da muka yi aure, kuma tattare da cewa in ba mu saya yanzu ba to nan gaba lokacin auren dole mu saye su da kudi ninkin ba ninkiya, to shin khumsi ya hau kan wadannan kayayyakin da muka ajiye su dan mu yi amfani da su?

A: Idan har kun saye su da riban kasuwancinku na shekara don ku amfana da su nan gaba, kuma ba su kasance abin bukatuwanku a wannan shakaran da kuka saya din ba, to akwai khumsi a cikinsu dai-dai da farashinsu matsakaici lokacin da shekarar ta yi, sai dai idan sun kasance a bisa al'ada suna daga cikin kayayyakin da ake sayansu kadan kadan ne da kuma ajiye su har lokacin bukata saboda rashin iya sayensu lokaci guda yayin da ake bukatuwa da su, kuma sun yi dai-dai da irin yanayinku, to anan ana kirga su a cikin abubuwan bukatuwa, don haka babu khumsi a cikinsu.
T842: Shin khumsi ya wajaba kan kudin da nake tarawa daga cikin albashina dan sayen kayayyakin aure?

A: Idan har ainin kudin (kudin da kansa) ne ka tara to wajibi ne ka fitar masa da khumsi idan shekara ta zagayo, ko da kuwa don sayen kayayyakin auren ne.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din