Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

ABUBUWAN DA KHUMSI BAI HAU KANSU BA
Ali Khamenei4

T843: Shin khumsi ya wajaba kan mutumin da wani abu ya saura a cikin kudinsa na shekara, tattare da cewa shekarar ta yi ne alhali yana da bashi akansa? Ko da yake yana da lokaci mai yawa na biyan wannan bashi nasa.

A: Bashi, shin na yanzu ko kuma wanda biyansa sai daga baya (wato za'a iya jinkirta shi) ba'a cire shi daga cikin riban shekara, sai dai bashin da aka karbe shi dan biyan bukatun shekarar da aka ci ribar, to shi kan ana cire shi daga cikinsa (riban shekara), don haka babu khumsi a cikinsa.
T844: Ina da wani gwargwado na riban kasuwancina na shekara wadanda khumsi ya hau kansu, to a dai-dai lokacin kuma ana bi na bashin wasu gwargwado na kudi, to tambaya a nan ita ce, shin zan iya ware kudin bashin da ake bi na daga cikin dukkan riban kasuwancin shekarar ko kuma? Tattare da cewa bashin da na karba din dan sayan mota ce ga kaina?

A: Ba'a kebance bashin da aka karba don sayen mota daga cikin riban kasuwancin shekara.
T845: Shin khumsi ya wajaba kan ma'aikatan da abin da suke da shi na kudi ya kan wuce abin da suke bukata na shekararsu? Tattare da cewa suna da basussuka a kansu.

A: Idan har bashin ya samo asali ne daga bashin kudin da aka karba a cikin wannan shekarar, dan biyan bukatu na yau da kullum na masarufi ko kuma wajen sayen wasu abubuwan bukatuwa na shekara (wato bashin kaya) to ana cire shi daga riban da ta saura, in kuwa ba haka ba to sauran abin da ya saura dole ne a cire masa khumsi.
T846: Ni na kasance ana bi na bashin wasu kudade, to idan shekara ta yi kuma mai kudin bai bukaci in biya shi ba, kana kuma ina da wani gwargwado na riban shekara, wato ina da daman biyan bashin, sai dai mai kudin bai bukaci hakan ba, to shin za'a iya ware wannan bashi daga riban shekara ko kuma?

A: Bashin da ya samo asali daga aron kudi ko kuma sayen wasu kayayyaki bashi, idan har an karbe shi saboda biyan bukatun kayan masarufi na yau da kullum na shekara, to ana cire shi daga cikin riban shekara, dan haka babu khumsi a cikinsa, to amma idan bai kasance bashi ne na bukatun kayan masarufi na shekara ba, ko kuma bashi ne na shekarun da suka gabata, to shi, ko da yake ya halatta a sarrafa riban shekara wajen biyansa (wato bashin), to amma idan har aka kai karshen shekara, ba a bayar ba to ba'a cire shi daga cikin riban shekara.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog