XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

AYYANA FARKON SHEKARA
Ali Khamenei4

T847: Mutumin da ya tabbatar cewa babu wani abin da zai saura a gare shi na daga riban kasuwancinsa na shekara har zuwa karshen shekara, face dai duk riban kasuwancin nasa zai tafi wajen abubuwan bukatuwa na masarufi a shekara, to shin duk da haka wajibi ne gare shi ya ayyana farkon shekarar Khumusinsa?

Shin ayyana farkon shekara wajibi ne? Kana mene ne hukuncin mutumin da bai ayyana wa kansa farkon shekara ba saboda yakinin cewa ba abin da zai saura a gare shi?

A: Ayyana farkon shekarar khumsi ba yana hannun mukallafi ba ne face dai tabbataccen al'amari ne da yake farawa daga lokacin da mutum ya fara kasuwanci ga wanda yake sana'ar kasuwanci, kana da zuwan lokacin girbi ga manomi, Kana daga lokacin karban albashi ga ma' aikata. Don haka lissafin farkon shekara da kuma shigowar shekara ba wani wajibi ne mai cin gashin kansa ba, face dai hanya ce kawai ta sanin abin da ya wajaba na daga khumsi, saboda haka yake wajaba to idan har ba abin da ya saura na daga riban kasuwancinsa, duk abin da ya samu ya sarrafa shi wajen abubuwan bukatunsa na shekara, to babu abin da ya wajaba a kansa.
T848: Shin miji da matan da suke hada albashinsu waje guda dan gudanar da ayyukan gida zai yiwu su yi amfani da shekaran khumsi guda?

A: Kowannensu zai kasance da lokacinsa na khumsi na daban ne (mai cin gashin kansa) dan haka wajibi ne ga kowannensu ya fitar da khumsin abin da ya saura na daga albashi da kuma kudin shigarsa na shekara a karshen shekarar khumsinsa.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din