Yau Shekaru Biyu Da Ta'addancin Sojojin Nigeriya A Zaria

12 Disamba 2017
A Nijeriya, dubun-dubatar magoya bayan Harkar Musulunci ne suka hau kwalta a cikin babban birnin Tarayya, Abuja suna masu kira ga Gwamnatin Buhari da ta gaggauta sakin Jagoran Harkar ta Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda take tsare da shi tun tsawon shekaru biyu da suka gabata. A rana mai kamar yau 12 ga Disambar 2015 ne Sojojin Nijeriya suka kaddamar da harin ta'addanci a kan Shaikh Ibraheem Zakzaky da magoya bayansa, inda suka kashe kusan mutum 1000 daga almajiransa, tare da kona wasu da ransu a cikin gidansa, cikin wadanda Sojojin suka kona da rai har da yayar Shaikh Zakzaky, Guggo Fatima 'Yar kimanin shekaru 70 a Duniya.
Tare da kashe 'ya'yan Malamin guda uku a gabansa, suka bude wuta a kansa da Mai dakinsa suka musu harbin kisa, har ta kai ma ga ya rasa idonsa guda daya, sannan suka dauke shi a baro suka tafi da shi da daruruwan almajirinsa.
Yau shekaru biyu kenan har yau Ana tsare da shi duk da rashin lafiyar da yake fama da shi da matarsa.
A lokacin da sojojin Nijeriya ke yin wannan ta'addancin a garin Zariya, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari na cikin garin Kaduna, ya halarci bikin gad'a, kuma gwamnan jihar Kaduna ba kawai bai sani bane, har ma ya zo Husainiyyah Bakiyatullah a yayin da sojojin ke bude wutan suka yi magana da su, bayan komawarsa ba jimawa Sojojin suka zo unguwar Gyallesu suka fara jefa bama-bamai da ababen fashewa a gidan Shaikh Zakzaky.
Gwamnatin Kaduna da bakinta ta sanar da cewa jami'anta sun taimakawa Sojojin Nigeria wajen bizne almajiran Shaikh Zakzaky da suka kashe a Zariya su kimanin 347 a cikin rami daya a kauyen Mando da ke bayan garin Kaduna.
Har yau ba a hukunta masu wannan aika-aikar ba, ba wani jami'in tsaro da ake tsare da shi ballantana a hukunta shi.
Sai ma cigaba da tsare masu raunin da Sojoji suka kama suka mikawa yan Sanda da ake yi a Kurkukun Kaduna da wasu da Ba su bayyana inda suke tsare da su ba.
Tuni wata babbar kotu a garin Abuja ta ba Gwamnatin Buhari umurnin ta gaggauta sakin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa daga rikewar da suke musu, su kuma biya su diyyar miliyan 50 tare da gina masa gida a duk inda suke bukata a Arewacin kasar nan.
Kimanin shekara guda da Wannan umurnin har yau Buhari da gwamnatinsa ba su saki Jagoran ba.
Mabiya Harkar Musulunci sun fara gudanar da Muzaharar nuna rashin amincewa da cigaba da tsare Jagoran yau a garin Abuja.
Ana sa ran Muzaharorin za su cigaba da gudana gobe Laraba da Alhamis a garin na Abuja.
Ga wasu daga hotunan Muzaharar ta yau.












.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved